Sunday 21 October 2018

Abubuwan dasuke bata sabon aure a kasar Hausa


Yankinmu na arewa ko kuma ace yankin hausa/Fulani ya kasance inda yafi koina mutuwar aure. A cikin al’ummar hausa/Fulani zakaga aure bashida martaba da kima sosai a idon wasu sabida yanda suke yanda sukaga dama dashi a duk lokacin dasuke so. Munsamu kanmu a wani lokaci da akanyi aure auren yamutu a cikin wata 3, Maza basu dauki saki wani babban abu ba sukanyi shi akan dalilin da bai kai ya kawo ba.


Wanan matsala takasance ta dami al’ummar mu. Saki abu ne wanda yake halal a musulunci amma dukda halarcinsa yakasance abu wanda Allah da Manzonsa basa sonshi. Illar saki yawuce kawai rabuwar ma’auratan, yana naso ne har izuwa dangi da sauran yan’uwan su.
Wanan matsala yawancinta ba a ciki gida ake samunta ba, ana samota ne tin daga waje kafin ayi aure. Sannan kuma akwai abubuwa dasuke kashe aure kuma wanda sai bayan anyi aure ake haduwa dasu.
Bari muyi bayanin kadan daga cikin matsaloli dasuke kashe aure a al’ummar hausa/Fulani

1.      Karya
Abu na farko dayake fara kawo matsala a acikin aure shine karya, zaka iya ganin Kaman cewa wanan ai bawani babban abu bane amma tabbas karya dazaka yita yiwa yarinya a waje kafin aure bayan tashigo taga labarin yasha bam-bam yanada matukar tasiri wajen Haifa muku matsala a cikin aure. Samari idan zasuje hira ko zance zai tabbatar ya fita fes-fes, zai tabbatar yatafi da kudi dayawa wanda zai bata alhali karfinsa bai kai yabada wanan kudi ba, watakila zai aro mota yatafi mata dashi.

Yanzu misali ace ma’aikaci ne mutum yanada albashin dubu hamsin (50) amma zai iya daukan dubu ashirin yabawa budurwa, sannan zai aro mota yaje wajenta, bata taba neman wani abu a wajensa tarasa ba duk tsadarsa. Sai azo ayi aure taga motar nan ba tasa bace kudinda yake bata yanzu bazai iya bata ba sabida yanada iyali yanzu, idan tanemi wani abu mai tsada ko kuid masu dan yawa  sai yace sai ya karbi adashi, tayaya baza’a fara samun matsala ba kanuna mata zaka iya kuma kazo ka kasa.

Abinda yafi shine kada kadinga yimata karya, idan aro mota kayi kafada mata wannan motar ba taka bace, idan ta nemi kudi masu yawa wanda bazaka iya bataba karka takura kanka sai ka samo kafada mata wallahi bakada shi zaka duba dai, kada kanuna mata kai mai kudi ne komai takeso zaka iya bata. To zaku gina soyayyarku akan gaskiya da gaskiya koda bayan kunyi aure tace kamata wani abu baka iya bata ba zata fahimci hakan.

2.      Kazanta/Rashin kula da gida
Wanan baya shafi mata bane kawai har maza ma, idan zaaje zance saurayi da budurwa kowa sai ya kure adaka, zai tabbatar kayansa masu kyau ne, yafesa turare sanan ya fito. Aure kuma zama za’ayi wanda zaku kwana tare ku tashi tare, bazai yiwu ace kowa yana cikinn kwalliya ba koda yaushe, amma yakamata kudinga kasancewa cikin tsafta koda yaushe kada kibari mijinki yaga kazantarki, kada kabari matarka taga kazantar ka. Ganin kazantar juna shine yakesa kuji kun ishi juna tin kafin ayi nisa sai azo afara zaman a hakuri har kowa yafara fito da abinda ke cikin ransa sai kuma kaga anata samun matsaloli karshe aure ya mutu arasa meye dalili tin farko ashe kazanta ce.

3.      Dangi da Yan’uwa
Yan’uwa da dangi suna daga cikin manyan abubuwa dasuke kashe aure a arewa, wani matsalar daga yan’uwan miji wani matsalan daga yan uwan mata. Wasu yan’uwan miji daga sunzo matar bata musu abunda sukeso ba shikenan zasu hau zaginta da sukanta, idan akayi rashin sa’a manya ma suka shigo shikenan saikaga ansa miji ya saki matarsa. Tsakaninsu basuda wata matsala amma sabida rigimarsu da yan’uwan mijin aure sai yamutu. Akwai wani bawan Allah da akasa ya saki matarsa kawai dan yan’uwan matar sun wulakanta yan uwan mijin, kawai suka sashi dole ya saki matarsa.

Yakamata aji tsoron Allah adaina  raba aure, musamman idan ba wani dalili ne mai karfi ba. Miji ko Mata kada ku bari ashiga tsakaninku kowani matsala zaku iya sasanta kanku basai wani ya shigo ba.




Tuesday 11 September 2018

Abubuwan dasuke kawo matsala ga ango da amarya





Bayan anyi aure zakaga soyayyar da miji yakema matarsa yaragu, zakaga yarage damuwa da’ita yarage nuna mata soyayya da kula, wasu sukan dauka dama haka abun zai kasance saboda haka basa damuwa. Tabbas wasu mazan suna ganin tinda kin riga kin aureshi ai shikenan bawani sauran soyayya dazai dinga nuna miki kuma abunda wasu ke cewa “ba’a campaign bayan anci zabe”.
Amma yawancin maza dalilai ne dakuma matsaloli daga wajen matan yakesa su zama haka. Mata su ke sa maza su daina nuna musu so da kauna bayan aure sabida wasu dabi’u dasuke farayi bayan anyi aure. Zamuyi bayanin kadan daga cikin wanan matsaloli.



1.      Rashin kwalliya.
Yawancin mata bayan angama biki ana tarewa watakila ace bayan angama cin amarci zakaga tadaina kwalliya a cikin gida sai zata fita, yawanci kuma bayan anyi aure akan dan jima ba’a fita ba, to ko kada ki manta kafin kuyi aure bai saba ganinki ba kwalliya ba, duk lokacinda zaku hadu sai kin tabbatarda kin yarda da kwalliyarki, to bayan aure kindaina kwalliya to sai ya dinga kallon abun wani iri zai dinga kallonki wani iri haka da bai saba gani ba. To daga nan sonki zai ragu a idanunsa. Ansani bazaki kasance cikin kwalliya ba koda yaushe shima kansa yasani amma sai kiyi kokarin yawaita kwalliyan da tsafta.

2.      Magana
Wasu matan zakaga basa tauna magana kafin su furta ta, wata tin kafin ayi auren ma dama haka take, kawai saboda soyayyar da yake mata ne na saurayi da budurwa sai yayita hakuri yana kauda kai. Amma bayan kunyi aure kinsani cewa mijinki bazai dauki magana marar dadi ba indai zaki dinga fada masa magana son ranki to mutuncin ki zai ragu a idonsa yaji ya daina sonki.

3.      Kazanta
Kazanta ta jiki data gida tanasa ango yafara gajiya da amaryarsa tin kafin suyi nisa, bai zama dole ya miki magana ba saboda amarya bata laifi amma abun na cikin ransa zaifada a cikin ransa ke kazama ce, to wanan zai rage miki kwarjini a idonsa. Kada ki bari ko tayaya mijinki yaga kazantarki.

4.      Rashin kula da baki
Indai akace anyi biki to amarya da ango zasuyita ganin baki, kullum zakaga gidan cike yake da baki, yan uwan amarya dana ango da abokanai duk zasuyita kawo ziyara, to wata batada dabi’ar kula da baki musamman idan suka kasance ba yan’uwanta bane ko kawayenta, indai bakin na mijinta ne sai kaga basa samun kula yanda yakamata. Wanan zaisa afara samun matsala tsakanin ango da amaryarsa.

Akwai abubuwa dayawa dasuke hada ango da amarya sabon aure kaga sun fara samun matsala, munyi bayanin kadan ne anan, muna bukatar raayoyinku kuma.


Monday 3 September 2018

Hotuna: Dan China ya musulunta ya auri bahaushiya


Akwai alaka mai karfi ta kasuwanci tsakanin mutanan Nigeria da yan kasar China, wanan alaka tayi karfi tawuce ta kasuwanci kawai inda ake samun auratayya atsakani. Wanan wani dan kasar China ne ya musulunta kuma ya auri bahaushiya agarin wase dake Jihar Plateau, Allah yabasuw zaman lafiya.


Sunday 2 September 2018

Dan Allah ku siya mun form din takarar shugaban kasa - Malam Tafida


Dan takarar shugabancin kasa Malam Hamidu Tafida, ya bukaci yan Najeriya miliyan daya (1) dasuyi dafifi wajen hada naira dari biyu biyu wajen siya masa form na neman takarar shugaban kasar Najeriya a jamiyyar (PDP).

Malam Tafida yayi wanan kira ne jiya a gain jalingo inda ya bayyana kudurinsa na neman takarar shugaban kasa a zabe dazaayi na shekara 2019.
Malam Tafida yayi alkawarin in aka zabe shi zai yi yaki da cin hanci da rashawa kuma zai kawo aiyuka da zasu kawo cigaba a kasa baki daya.
Malam tafida dai ma,aikacin karamar hukumar jalingo ne dake Jahar Taraba




Saturday 14 July 2018

Ina son inyi aure - Aliko Dangote




Babban dan kasuwa kuma hamshakin mai kudi kuma wanda yafi kowa kudi  a Africa wato Alhaji Aliko Dangote,  yace yana da shirin sake aure domin ya zauna ya huta kaman yanda kowa yake.


Alhaji Aliko Dangote ya bayyana cewa shekarunsa a yanzu sunkai sittin (60) shiba yaro bane ya kuma nuna cewa harkokinsa ne na kasuwanci suka hanashi ya zauna da matan daya aura, yace bai kamata ka ajiye mataba alhali bakada lokacinta.

Dangote dai yace bayan ya kammala aikin gina matatar man fetur dinsa zai yi aure ya huta.
Tini dai aka samu wasu mata dasuka nuna cewa sufa sun dade suna kaunarsa kuma a shirye suke a daura aure, shin kana ganin wanan so ne nagaske ko akwai ayar tambaya?

Tuesday 26 June 2018

Abinda zaka yi idan yarinya tace bata sonka



Wasu sukan shiga damuwa bayan sun bayyana sirrin zuciyarsu a wajen mace kuma yazamana basu samu karbuwa ba a wajenta ba , dalilai biyu suke sa mace taki amincewa da namiji, na farko shine idan Allah bai hada jininku ba, indai Allah bai hada jininku da yarinya ba duk abunda zakayi bazaka burgeta ba. Abu nabiyu wani dalili ko matsala ce daga gareka yasa bata son ka, ko baka iya saka kaya ba ko baka iya Magana ba da dai sauransu.


·         Idan ka bayyana wa mace kana sonta bata amince dakai ba sai ka tsaya ka duba daga ina matsalar take? Abubuwan dazaka duba sune lokacin da zaka je gurinta wani irin kaya kasaka? Mata nason gayu suna son samari yan gayu, idan kayan daka saka daza fara zuwa wajenta bamasu kyau bane to sai ka duba wanan ga gyara.

·         lokacin dakake magana da’ita zaka fahimci idan bata jin dadin maganarka ko kuma kana fadan wani abu wanda yake bata mata rai, to dole ka canza salon maganarka zuwa yanda ka tabbatar zataji dadinsa.

·         Atakaice dai ka lura da ta’ina matsalar take idan daga kaine sai ka gyara ka sake salo watakila ta karbeka.


·         Idan kuma ka fahimci matsalar badaga kai bane kawai itace dai bata sonka ko kuma tana da wani wanda take so, to idan kayi iya kokarinka sai ka hakura ka kyaleta kawai kanemi wata, indai yarinya ta nuna bata sonka abinda yafi kawai ka hakura sabida zaka zama kana ta shan wahala akanta ita kuma bata yabawa. Ka hakura ka nemi wata akwai mata dayawa watakila wata ma tana sonka takasa gayamaka.



Monday 25 June 2018

The reason you don't need any job




There are many write ups that discussed about comparison between jobs and self-owned business. But the fact is there is nothing to compare, self-owned business is far better than any job one could get. However, getting a job is easier that starting a business but like they say the harder the way the more chance of becoming successful.

Starting a business requires a lot of things, capital as many believes is not the first requirement for starting a business but dedication, commitment and financial discipline are the most vital traits that anyone starting any business should have. Anyway we will discuss about how a business man should be in our coming articles, let us get back to our topic.

We will discuss here the reasons you should start your business instead of securing a job.

1.     When you are working for somebody, you don’t have the time of your own, your boss owns your time and he schedules it, you cannot do anything or go anywhere without seeking for your boss approval. If you have your business, you can go out anytime you like and come back anytime you wish.

2.       The most painful part of being an employee is you are working tirelessly, putting all your strength, effort and commitment towards making someone rich, the funny thing is while you are busy making money for him he is busy planning how to spend it.

3.       If you have your own business, there is no limit to what you can earn, you can as much as possible without waiting salary from anyone.

4.       If you have your own business, you don’t have to face the risk of dismissal or getting fired, if you have a job, no matter how good it is and how they are paying you, you have no certainty and guarantee over it, you will be always working hard, always in fear of getting fired.  

So as a graduate or anyone who wants to start making money to make a living, you need to think and think again and make a wise choice between the two

Friday 22 June 2018

Abinda yasa Shugaba Buhari kuka jiya



Hawaye sun zubo a fiskar Shugaban kasa Muhammadu Buhari a jiya lokacin da yakai ziyara ta jaje akan gobarar data tashi a kasuwar Azare dake Jihar Bauchi wanda tayi sanadiyar konewan shaguna dasuka kai 750.
Shugaba Muhammadu Buhari

Shugaba Buhari yakai ziyarar ne domin ganewa idonsa barnar da asarar da gobarar ta jawo a kan yan kasuwan.

Shugaba Buhari yace gobarar dai kaddara ce daga Allah, kuma ya jajantawa yan kasuwan sannan ya tabbatar da cewa Gomnatin tarayya zatayi iya kokarinta wajen taimakawa wadanda abun ya shafa.
Gwamnan Jihar Bauchi, Muhammad Abubakar da Sarkin Katagum, Alhaji Umar Faruk sun nuna godiyarsu da ziyarar da Shugaba Buhari ya kawo musu.

Sarkin Katagum, Allhaji Umar Faruk, ya nemi taimakon gomnatin tarayya wajen kara inganta tsaro a hanyoyin Azare – Potiskum sabida yawan fashi da akeyi a hanyar.

Thursday 21 June 2018

The lies our teachers told us about jobs




When we were in secondary school days, we were frequently reminded by our teachers that our fate depends on our academic performances, I could recall there was a teacher who once told us that “If you graduate with good grades you will all get a good job and if you fail to do so you will not get a good one” but we couldn't ask him about his own grades and how he ended up teaching secondary school students.



In university they gave us the impression that if you don’t have a degree you will never make it in life or your making in life depends on your class of degree, but after graduating with the good grades we found out things are not exactly as we were led to believe, jobs are hard to get. I came across many graduates that have graduated 6 to 8 years without job most of them have given up already. Most graduates prefer having multiple copies of their CVs and submitting them from one office to another in search of jobs which most of them eventually dont get.

So now, do you choose to spend many years searching for a job or you wish to make any bold step to change your life for better? a question you should ask yourself. But honestly, after all the hardship you experience in schools, after all you have been through, you don’t deserve this treatment.

Here is an advice for you, Why don’t you start a business whether small or big, Business is the way you make a living without waiting for someone to employ you, to be self employed is the best way to live a happy life, nobody tells you when to come and go, you have absolute freedom and most importantly you control your income. It has been confirmed that most graduates that choose to start their own business and make their own money tend to be more successful than those who secured a job, because with a good business you can earn 5 times what any civil servant can earn in the whole month. So forget about your class of degree and face real life.

We will tell you how to start your own business in our next article, keep in touch.


ENGLISH ARTICLES coming your way




ZINARIYA is a blog that was created to satisfy the needs of public as regards to rich and reliable contents concerning all aspects of life. Being based in northern Nigeria we thought it would be better if we use the predominant language here with is Hausa language. But we later on agreed that a blog containing such vital and imperative information shouldn’t be restricted to only one part of the country, so we decided on using a central language that everybody does understands and we finalized on Nigeria’s official language that is English language. So keep in touch always as you we will be providing you with our unique English based articles, Cheers..

Tuesday 19 June 2018

Yanda ake karbar numbar yarinya cikin sauki



Tambayar mace tabaka numbarta abune mai yuwa, musamman idan baka sababa. A duk lokacin da kake kokarin yin hakan sai zuciyarka ta kada kuma sai kayi tunanin; to yazanyi idan tace bazata baniba? Wani zaice maka kawai katambayi kawarta tabaka, koka tambayi kaninta ko wani dan uwanta. Wannan duk hanyoyi ne zaka iya samun numbarta amma kasan idan ita tabaka da kanta abin zaizo maka da sauki, kuma baka bukatar dada gabatar da kanka a gurinta a yayin da kakirata.
A wannnan bayana zakaji hanyoyi uku da akebi akarbi numbarta cikin sauki.




1- Kaje wajenta ku gaisa, sannan  kayabeta  ita da kayan da tasaka, domin kasan cewa babu abinda mace takeso fiye da ayaba mata. Amma kafin kaje gurin nata katabbatar cewa wajen yayi dai dai da har zaku dan iya tattaunawa.

2- Idan zaka karbi numbarta, kada kace mata bani numbarki, aa kayi amfani da dabaru irin namaza, misali zan iya samun numbarki ko text na dan rika yimiki, kodai wani dan wasa amma bawai kawai katambaya kai tsayeba. kuma idan zaka kaje katafi da wayarka kamika mata tasaka  maka da kanta.



3- Bayan ta saka maka numbarta zaka iya yimata text message dan gajere, misali “ thanks for giving me your number, you are beautiful”

 Kagwada wadan nan hanyoyi, zakaga abin mamaki.


Saturday 16 June 2018

HOTUNA: Hotunan sallah daga fadar shugaban kasa

Shugaban kasa Muhammadu Buhari yana taya mutanen Nijeria murnar zagayowar karamar sallah, Shugaba Buhari yayi sallan idi ne a Mambilla barracks dake garin Abuja. Bayan sallan idi ne iyalai da ministocinsa da sauran mutane suka kai masa ziyarar sallah afadar shugaban kasa dake Aso rock.












Thursday 14 June 2018

Sarkin Musulmi ya tabbatar da ganin watan shawwal, duba garuruwan da aka gani


Mai alfarma Sarkin musulmi Muhammad Sa'ad Abubakar na III ya tabbatar da cewa anga Jaririn watan shawwal sabida haka ya bayyana cewa gobe juma'a 1 ga watan shawwal, 15 ga watan yuli a matsayin ranar sallah a Najeriya.


Sarkin musulmin na Najeriya ya ce an ga sabon watan na Shawwal a garuruwa da dama na kasar da suka hada da Sakkwato da Kano da Zaria da Maiduguri da Jos da sauransu.

Hakan shine ya kawo karshen azumin watan Ramadan.

Source: BBC HAUSA