Saturday 14 July 2018

Ina son inyi aure - Aliko Dangote




Babban dan kasuwa kuma hamshakin mai kudi kuma wanda yafi kowa kudi  a Africa wato Alhaji Aliko Dangote,  yace yana da shirin sake aure domin ya zauna ya huta kaman yanda kowa yake.


Alhaji Aliko Dangote ya bayyana cewa shekarunsa a yanzu sunkai sittin (60) shiba yaro bane ya kuma nuna cewa harkokinsa ne na kasuwanci suka hanashi ya zauna da matan daya aura, yace bai kamata ka ajiye mataba alhali bakada lokacinta.

Dangote dai yace bayan ya kammala aikin gina matatar man fetur dinsa zai yi aure ya huta.
Tini dai aka samu wasu mata dasuka nuna cewa sufa sun dade suna kaunarsa kuma a shirye suke a daura aure, shin kana ganin wanan so ne nagaske ko akwai ayar tambaya?

No comments:

Post a Comment