Tuesday 26 June 2018

Abinda zaka yi idan yarinya tace bata sonka



Wasu sukan shiga damuwa bayan sun bayyana sirrin zuciyarsu a wajen mace kuma yazamana basu samu karbuwa ba a wajenta ba , dalilai biyu suke sa mace taki amincewa da namiji, na farko shine idan Allah bai hada jininku ba, indai Allah bai hada jininku da yarinya ba duk abunda zakayi bazaka burgeta ba. Abu nabiyu wani dalili ko matsala ce daga gareka yasa bata son ka, ko baka iya saka kaya ba ko baka iya Magana ba da dai sauransu.


·         Idan ka bayyana wa mace kana sonta bata amince dakai ba sai ka tsaya ka duba daga ina matsalar take? Abubuwan dazaka duba sune lokacin da zaka je gurinta wani irin kaya kasaka? Mata nason gayu suna son samari yan gayu, idan kayan daka saka daza fara zuwa wajenta bamasu kyau bane to sai ka duba wanan ga gyara.

·         lokacin dakake magana da’ita zaka fahimci idan bata jin dadin maganarka ko kuma kana fadan wani abu wanda yake bata mata rai, to dole ka canza salon maganarka zuwa yanda ka tabbatar zataji dadinsa.

·         Atakaice dai ka lura da ta’ina matsalar take idan daga kaine sai ka gyara ka sake salo watakila ta karbeka.


·         Idan kuma ka fahimci matsalar badaga kai bane kawai itace dai bata sonka ko kuma tana da wani wanda take so, to idan kayi iya kokarinka sai ka hakura ka kyaleta kawai kanemi wata, indai yarinya ta nuna bata sonka abinda yafi kawai ka hakura sabida zaka zama kana ta shan wahala akanta ita kuma bata yabawa. Ka hakura ka nemi wata akwai mata dayawa watakila wata ma tana sonka takasa gayamaka.



No comments:

Post a Comment