Thursday 14 June 2018

Sarkin Musulmi ya tabbatar da ganin watan shawwal, duba garuruwan da aka gani


Mai alfarma Sarkin musulmi Muhammad Sa'ad Abubakar na III ya tabbatar da cewa anga Jaririn watan shawwal sabida haka ya bayyana cewa gobe juma'a 1 ga watan shawwal, 15 ga watan yuli a matsayin ranar sallah a Najeriya.


Sarkin musulmin na Najeriya ya ce an ga sabon watan na Shawwal a garuruwa da dama na kasar da suka hada da Sakkwato da Kano da Zaria da Maiduguri da Jos da sauransu.

Hakan shine ya kawo karshen azumin watan Ramadan.

Source: BBC HAUSA

No comments:

Post a Comment