Bayan anyi aure zakaga soyayyar da miji yakema matarsa
yaragu, zakaga yarage damuwa da’ita yarage nuna mata soyayya da kula, wasu
sukan dauka dama haka abun zai kasance saboda haka basa damuwa. Tabbas wasu
mazan suna ganin tinda kin riga kin aureshi ai shikenan bawani sauran soyayya
dazai dinga nuna miki kuma abunda wasu ke cewa “ba’a campaign bayan anci zabe”.
Amma yawancin maza dalilai ne dakuma matsaloli daga
wajen matan yakesa su zama haka. Mata su ke sa maza su daina nuna musu so da
kauna bayan aure sabida wasu dabi’u dasuke farayi bayan anyi aure. Zamuyi
bayanin kadan daga cikin wanan matsaloli.
1. Rashin
kwalliya.
Yawancin mata bayan angama biki ana
tarewa watakila ace bayan angama cin amarci zakaga tadaina kwalliya a cikin
gida sai zata fita, yawanci kuma bayan anyi aure akan dan jima ba’a fita ba, to
ko kada ki manta kafin kuyi aure bai saba ganinki ba kwalliya ba, duk lokacinda
zaku hadu sai kin tabbatarda kin yarda da kwalliyarki, to bayan aure kindaina
kwalliya to sai ya dinga kallon abun wani iri zai dinga kallonki wani iri haka
da bai saba gani ba. To daga nan sonki zai ragu a idanunsa. Ansani bazaki
kasance cikin kwalliya ba koda yaushe shima kansa yasani amma sai kiyi kokarin
yawaita kwalliyan da tsafta.
2. Magana
Wasu matan zakaga basa tauna magana
kafin su furta ta, wata tin kafin ayi auren ma dama haka take, kawai saboda
soyayyar da yake mata ne na saurayi da budurwa sai yayita hakuri yana kauda
kai. Amma bayan kunyi aure kinsani cewa mijinki bazai dauki magana marar dadi
ba indai zaki dinga fada masa magana son ranki to mutuncin ki zai ragu a idonsa
yaji ya daina sonki.
3. Kazanta
Kazanta ta jiki data gida tanasa ango
yafara gajiya da amaryarsa tin kafin suyi nisa, bai zama dole ya miki magana ba
saboda amarya bata laifi amma abun na cikin ransa zaifada a cikin ransa ke
kazama ce, to wanan zai rage miki kwarjini a idonsa. Kada ki bari ko tayaya
mijinki yaga kazantarki.
4. Rashin
kula da baki
Indai akace anyi biki to amarya da
ango zasuyita ganin baki, kullum zakaga gidan cike yake da baki, yan uwan
amarya dana ango da abokanai duk zasuyita kawo ziyara, to wata batada dabi’ar
kula da baki musamman idan suka kasance ba yan’uwanta bane ko kawayenta, indai
bakin na mijinta ne sai kaga basa samun kula yanda yakamata. Wanan zaisa afara
samun matsala tsakanin ango da amaryarsa.
Akwai abubuwa dayawa dasuke hada ango
da amarya sabon aure kaga sun fara samun matsala, munyi bayanin kadan ne anan,
muna bukatar raayoyinku kuma.
No comments:
Post a Comment