Friday 22 June 2018

Abinda yasa Shugaba Buhari kuka jiya



Hawaye sun zubo a fiskar Shugaban kasa Muhammadu Buhari a jiya lokacin da yakai ziyara ta jaje akan gobarar data tashi a kasuwar Azare dake Jihar Bauchi wanda tayi sanadiyar konewan shaguna dasuka kai 750.
Shugaba Muhammadu Buhari

Shugaba Buhari yakai ziyarar ne domin ganewa idonsa barnar da asarar da gobarar ta jawo a kan yan kasuwan.

Shugaba Buhari yace gobarar dai kaddara ce daga Allah, kuma ya jajantawa yan kasuwan sannan ya tabbatar da cewa Gomnatin tarayya zatayi iya kokarinta wajen taimakawa wadanda abun ya shafa.
Gwamnan Jihar Bauchi, Muhammad Abubakar da Sarkin Katagum, Alhaji Umar Faruk sun nuna godiyarsu da ziyarar da Shugaba Buhari ya kawo musu.

Sarkin Katagum, Allhaji Umar Faruk, ya nemi taimakon gomnatin tarayya wajen kara inganta tsaro a hanyoyin Azare – Potiskum sabida yawan fashi da akeyi a hanyar.

No comments:

Post a Comment