Sunday 10 June 2018

Abubuwan dasuke sa budurwa ta daina daukar wayarka


Samari da yammata suna amfani da wayoyinsu wajen kiran juna ayi wa juna kalaman soyayya kuma suji ya masoyan su suke, wasu zakaga suna waya yafi sau 5 a rana, wasu masoyan idan suka fara waya sai suyi awa suna magana batare da kowa yakosa ba. Kana kiran budurwarka ko takiraka kuyi awanni kuna waya rana tsaka sai kaga ta daina kiranka ko kuma ta rage, idan ka kira ba koyaushe take dauka ba to akwai dalili, ga wasu daga cikin dalilan:


1.      Idan kuna waya da budurwaka kada ka dinga damunta da hirar duniya kawai, hirarka tafi yawa akan gayamata yanda kake sonta, kullum kayita gayamata kana sonta bazata gaji ba, koda kaji tana cemaka tagaji dajin hakan acikin zuciyarta tana jin dadi. Hirarku tafi karkata ga soyayya da abunda yashafeku idan kacika bata hirar duniya zataji matsayinku da rediyo dayane.

Karanta:www.zinariya.com.ng/2018/06/dalilai-4-dasuka-saka-ta-daina-sonka.html?m=1

2.      Idan kuna waya karka dinga katseta lokacin da take magana, kajira tagama magana sai kaima kayi, idan kana katseta zatazo tafara jin haushin hakan harta zo ta daina daukar wayarka.

3.      Yanada kyau kafin ka kirata kadan yi tinanin mezaku yi magana akai, idan yarinya tana sonka sosai shine komai kafada zataji dadinsa amma idan son da take maka ba sosai bane idan ka kirata kana kame-kame sai kaga kafin bazaku wuce yan mintuna kadan ba ta kasha wayarta wasu lokutan ma taki daukar wayarka.

4.      Idan kuka gama waya kada yazama kana rigata kashe waya, ka barta ta kashe dakanta, wata zataga dama jira kake a gama kenan shiyasa kafin ku gama sallama ka kashe.





www.zinariya.com.ng/2018/06/dalilai-4-dasuka-saka-ta-daina-sonka.html?m=1

No comments:

Post a Comment