Sunday 10 June 2018

Manyan dalilai 4 dazasu sa budurwarka ta daina sonka






Soyyaya tana dadi idan aka dace, tana iya zama akasin haka idan aka samu matsala, lokuta dayawa namiji yakan samu karbuwa a wajen mace sufara soyayya, bayan wani dan lokaci kadan kuma sai kaga ta daina sonsa. Wani lokacin kai da kanka zaka fahimci dalilin dayasa ta daina sonka wani lokacin kuma bazaka gane dalilin dayasa ta daina sonka ba. Zamuyi bayani akan wasu daga cikin dalilan dasuke saka mace ta daina son namiji.





1.      Bambamcin ra’ayi
Wasu masoyan zakaga ra’ayinsu akan al’amura yana banbanta, duk abinda kace kana so sai kaga baka so, duk abunda take so sai kaga bakaso, to anan idan daya bai janye nasa ra’ayin ba sai kaga ana samun yar matsala karama da kai bazaka dauketa wani abu ba amma shi so abu ne dayake shiga ba shiri kuma yake fita duk sanda yaga dama, indai kuna yawan samun irin matsala haka to bazatasan lokacin da zataji sonka yaragu a ranta ba.


2.      
Rashin kula
Mace nason kula, duk lokacin da zata shiga wani damuwa yazamana kafita damuwa, damuwan da zaka nuna mata shi zaisa tadinga ji aranta duk wata matsalarta taka ce, wasu zakaga basuda kula sai yaganta cikin damuwa bazai nuna damuwarsa sosai ba akan damuwarta, daga yadan tambaya sau daya shikenan. Akwai wani saurayi dasuke soyayya da wata, to kwatsam wata rana sai wani abu yasameta yazo tana kuka kawai sai yayi tafiyarsa haka tacigaba dakuka har tagaji, sai daga baya take gayamasa bataji dadin abun da yamata ba, yatafi yabarta tana cikin matsala tafiyar dayayi shi yasa kukan ta yakaru, tindaga wanan lokaci ta daina kulashi sosai suka fara samun matsala. Indai baka nuna wa mace kula kabar wata kofa da duk lokacin data samu mai bata wanan kulan zai shige kuma yayi waje dakai.



3.      Rashin kyauta
Ko budurwarka tana tambayanka kudi ko bata tambayanka yakamata kadinga yimata kyauta lokaci-lokaci, ita zuciya tana son mai kyautata mata ko bata sonka idan kana yimata kyauta lokaci lokaci zataji tafara sonka, ba sai lallai kudi ba, akwai abubuwa dazasufi burge mace akan kudi misali chocolates. Matsalar wasu ke wuce gona da iri, akwai yarinyar da ita ba mai son yawan karban abun samari bane, inka fahimci haka to bakoyaushe zaka dinga dunkulo kudi da sauran abubuwa kana bata ba, wata zata dauka kana son nuna mata kudi ne, daga tafara tinanin haka kuma shikenan mutuncinka zaifara raguwa a wajenta.

4.      Yawan kula yammata
Duk son da mace take maka indai kanda kule-kule da tara yammata to zata daina sonka, mata nada kishi, indai zakace kana sonta to tana tsammanin kasota ita kadai, wata idan tafahimci kana da son yammata zataga kai ba wanda zata rike bane dole zata daina sonka.

No comments:

Post a Comment