Kudin yin karatu a university a kullum sai karuwa yake kuma dalibai nata karuwa, guraben karatun sonata raguwa. A manyan universities na duniya, dalibai nada damar yin karatu a bashi (student loan debt) wanda zaka biya bayan ka kammala karatunka. Zinariya zata rika kawo muku damarmakin yin karatu a wasu daga cikin universities dake Europe wanda indai kacika sharudansu kwata kwata ba’a biyan kudin makaranta. (Tuition free)
Wadan nan damarmaki
yan uwanmu yan kudancin Nigeria sun dade suna morarsu. Amma mu yan arewa
saboda karancin amfaninmu da internet bamu san dasuba.
A yau zamu maida hankaline a kan universities din
dake kasar Norway.
Norway
Kasar Norway tashahara da karbar baki yan kasashen waje wadanda sukazo domin cin moriyar dumbin
ilimin da allah ya bawa kasar. Universities din gwamnati a kasar Norway basa
cajar kudi a gun dalibi ko dan kasa ko kuma bako. ( Tuition free). Daga zarar
kasami nasara sun daukeka to gwamnatice zata dauki dawainiyar karatunka.
Zinariya ta kawo muku jerin sunayen universities 9
da zaka samu damar yin karatu kyauta batare da kabiya kudin makarantaba. (
Tuition free). Abin dadi ana shine ko
digiri na daya zakayi ko digiri na biyu zakayi duk kyautane. (Bachelor degree
ko masters degree)
Dukkan wadan nan universities da aka jero basa
karbar kudin makaranta daga hannun dalibi ko bako ko dan kasa. Domin samarwa
kanka gurbin karatu kawai sai ka latsa sunan makarantar dakake so, zai maidaka
shafin makarantar inda zaka samu damar neman gurbin karatu.
Lokaci zuwa lokaci zamu rika kawo muku damarmakin
yin karatu kyauta universities dake gida
ko kasashen waje. Sai kucigaba da kasancewa da shafinku na zinariya.com.ng
Domin neman Karin bayani sai katun tubemu ta ashen
comments dake kasa domin samun damar yin tambaya ko Karin bayani.
No comments:
Post a Comment