Thursday 14 June 2018

Wanan itace mai shari'ar data yankewa tsofaffin gomnoni shekaru 14 a gidan yari, karanta kaji dalilin dayasa batada tsoro




Mai shari’a Adebukola Banjoko mace ce mai kamar maza da batada tsoro ko shakka na wani, itace mai shari’ar data yankewa tsofaffin gomnoni guda biyu hukuncin shekaru 14 a gidan yari babu zabin tara bisa zargin almundahana da babakere da dukiyar jihohinsu.


Tsofaffin gomnonin sune Jolly Nyame, tsohon gomnan jihar Taraba dakuma Sen. Joshua, tsohon gomnan jihar Plateau.

Karanta:http://www.zinariya.com.ng/2018/06/wanan-itace-mai-shariar-data-yanke

Ankama Jolly nyame da laifuka 27 a cikin 41 da ake tuhumarsa dasu. An kama shi da almundahana na kudaden da suka kai naira biliyan daya da miliyan dari shida da hudu (N1.64bn) a lokacin da yayi gomna shekara ta 1999 zuwa 2007.



Karanta:www.zinariya.com.ng/2018/06/abinda-buhari-yace-zaiyi-wa-matasa.html?m=1

Shikuma Joshua Dariye ana tuhumarsa da laifuka 23 ciki harda karkata kudin jiharsa dasuka kai naira biliyan daya da miliyan dari shida da biyu (N1.62bn)
Mai shari’a Banjoko tace babu wani sassauci ko rangwame akan cin hanci da rashawa.

No comments:

Post a Comment