Sallah biki ne na duk musulmai a duk fadin duniya da
akeyi bayan kamala azumi na watan Ramadan, kuma lokaci ne da ake dinka sababbin
kaya domin da dafe dafe domin murnar irin wanan lokaci. Lokaci ne kuma da ake
ziyaran yan uwa dakuma nuna wa yara muhimmancin iyali da yan uwa. Wadanan sune abubuwan
daya kamata ka shirya wa bikin sallah:
1.
Kayan
sallah
Sunnah ce mai kyau dinka sababbin
kaya da za’a saka ranar sallah, idan babu kuma sai ka samu kayanka masu kyau
kasaka aje sallar idi. Sababbin kaya da zaka gani a ko’ina shi zai kara nuna
maka farinciki da annashuwa da mutane ke ciki a wanan lokaci.
2.
Tuwon
sallah
Idan ance tuwon sallah ba ana nufin
sai lalle tuwo ba, sallah lokaci ne da ake girke girke dayawa sabida gida, yan
uwa, makota da baki. Yakamata ayi girke girke sabida aci a koshi a wanan lokaci
musamman dayake anyi wata guda ba’aci abinci da rana ba. Wadanan girke girke
yakamta ace sun sami tagomashi na wasu kaji da zasu kara wa abincin armashi.
3.
Wuraren
ziyara
Yakamata ayi ziyaran yan uwa da
abokan arziki a wanan lokaci, bayan ziyara ta yan uwa akwai wurare da shakatawa
da ake halarta a lokacin bukuwan sallah, yanada kyau akai iyali da yara irin
wadanan wajejen domin su sami nishadi sosai kuma su san cewa lalle a lokacin
sallah ake.
4.
Samun
lokacin iyali
Sallah Lokaci ne na hutu, yakamata a
zauna da iyali kowa da kowa aci abinci tare ayi hira da juna, koda ba’a samu
ana yin haka ko da yaushe amma a lokacin sallah yanada kyau mutanen gida su
zauna su samu lokacin juna.
Shawara takarshe kaman yanda bahaushe
yace sallah mai biki daya rana tawuce tabar wawa da bashi, kada ka tara wa
kanka bashi sabida kanaso lalle sai ka yi abunda yafi karfinka, ayi komai dai
dai yanda baza’a takura ba. Allah yakarbi ibadunmu, Allah ya maimaita mana.
No comments:
Post a Comment