Shugaban kasa
Muhammadu Buhari yace gomnatinsa tana kokarin shawo kan matsalolin matasa da sauran
matsolin dasuka damu kasar baki daya, yayi wannan jawabi ne a yau daya karbi bakoncin
kungiyar matasa da kuma yan kungiyar wasa na fim da sauransu a taron shan ruwa
wanda fadar shugaban kasa ta gayyacesu.
Shugaban ya kara da cewa gomnatinsa na kokarin kyautata
rayuwar matasa ta bangarori daban daban yanda zasu tsaya da kafafunsu har su
samu daman daukan wasu aiki. Yace Gomnatinsa zata cigaba da kawo hanyoyi da
zasu inganta.
Shugaba Buhari ya bawa matasan shawaran suci gaba da
neman ilimi a kowani mataki domin cigabn al’umma.
Shugaban ya kuma jaddada muhimmanci na wayarwa da yan
kasa hankali akan yin katin zabe musamman da lokacin zabe yake karatowa.
A yayin jawabinsa a madadin kungiyoyin, Mr Kunle yayi
godiya ga shugaba Buhari sabida kokarinsa wajen habaka tattalin arzikin kasa da
kuma cigaba ga al’ umma kuma yayi alkwarin jagorantan matasa wajen nuna goyon
bayansu ga Gomnatin shugaba Buhari domin cigaban kasa.
No comments:
Post a Comment