![]() |
Photo credit: Pexels.com |
Masoya suna kasancewa
cikin jin dadi aduk lokacin dasuke tare suna hira da juna, saurayi yazo wajen
budurwarsa hira ko zance al’ada ce da take da asali akasar hausa, amma zamani
ya kawo hanyoyi dayawa da zakayi hira da budurwarka batare da kun hadu ba. Hirar
tanada fa’ida sosai wajen ku san junan ku da kara shakuwa tsakaninku , sai dai
hirar da zakayi da budurwarka tanada ka’idodi dazaka bi. Hirar dakakeyi dakai da
abokinka namiji tasha ban ban da hirar daya kamata kayi da mace. Shiyasa a lokuta
da dama maza ke samun matsala wajen kasa shawo kan yarinyar da suke kauna.
Hakan yasamo asali ne tun lokacin kuruciya. Maza na rayuwa da yan uwa nasu maza
har takai sun saba da yanayin hirar da suke a tsakaninsu. Basu san yanda ake
hira da mace ba har suja hankalita.
A wannan bayani zaka
koyi abubuwa kamar haka:
· Ingantacciyar hanyar da
ake yiwa mace Magana
· Banbanci tsakani hira da
mace da kuma hira da namiji.
Yanayi hirar dake gudana
tsakanin namiji da namiji dan uwansa. mafi yawanci hira ce da bata wuce hirar wasan
kwallon kafa, hirar motoci, hirar siyasa, hirar mata, hirar kudi, Sana’a,
kasuwanci ko aikin office
Hira kuma da mace take da yar uwarta bata wuce
hirar Hirar Fina finai, tsegumi, hirar soyayya da samari, hira akan kwalliya,
Hira akan kayan kawa da ado, da dai sauransu
Idan kaduba zakaga hirar
da mace take da yar uwarta ya banbanta da hirar da namiji yake da dan uwansa.
idan harkace zakayi amfani da yanayin hirarka kai da dan uwanka namiji to
bazaka taba samun nasaraba, bazata taba son kaba, kullun idan kana mata hira
zataji duk kadameta ta Allah Allah kagama katafi.
To wai shin yama hirar
yakamata ta kasance? Hira tsakanin saurayi da budurwa ta sha ban ban ta wurare
dayawa, yana da kyau kaduba yaanyin irin labaran datake so sai kadinga bada
hankalimka wajen. Ga bayanin yanda zaka yi hira da budurwarka :
1. Kagane irin Labaran datake so.
Mata suna son saurayi
mai hira, mai bada labarai masu dadi. Dukanmu muna da labarai masu dadi da
yakamata mubawa wanda mukeso. Babban abin kula anan shine katabbatar cewa ba
irin labaran kane kai da abokinkaba. Misali babu yanda zakayi ka birge mace da
hirar siyasaba, ko hirar kwallon kafa. Kai zaka gane irin labaran da budurwarka
ko wacca kakeso takeson taji sai kadinga bata su.
2. Kada kacika yi mata
tambayoyi
Idan kasami damar yin
hira da mace, kayi kokari wajen rage tambayoyi acikin hirar taku. Idan kacika
mata tambayoyi sai taji kamar dan jaridane ya titsiyeta ya yake mata tambayoyi.
Haka zaisa tayi saurin kosawa dakai. Kayi kokarin bata labarai amma ka rage
tambayoyi a cikin hira taku.
3. Ka nemi dalilin dazai hadaku
Anan abinda nake
nufi shine kayi kokari ka gano abinda tafi so. Haka zai kaika ganemo duk wasu
labarai da suka shafi wannan abin. Misali, Idan ka fahimci ita ma’abociyar
kallon film din india ce to kaima yakamata kafara kallon film din india saboda
kasami abinda zaka fada mata idan kuna hira.
4. Kada ka dinga yimata
hira ko tambayoyi akan samarinta
Yawancin mata zakaga
suna da samari dasuka wuce daya, idan kazoo wajenta kada kadinga damuwa
dayimata hira ko maganar data shafi sauran samarinta, hakan shi zaisa taga
girmanka kuma tagane kai ba me takura bane, mata kuma dama basa san mai takura.
Akwai hanyoyi dayawa dazakayi hira da budurwarka, Wadanan
kadan ne daga cikin mukayi bayani anan.
No comments:
Post a Comment