Sunday, 20 May 2018

Karanta kaga amfanin yayan itatuwa a jikin dan adam


Shin kana cin yayan itatuwa? sau nawa kakeci a rana? Da wani lokaci kakeci? Bincike yanuna cewa mutanen farko wanda ake kiran lokacin da turanci (stone age) mutane ne wanda suke cike
da koshin lafiya, cututtuka sunyi karanci a wancan lokaci kuma mutanene ne wadanda suka samu shekaru masu yawa a duniya.

A wancan lokaci abinci da ake amfani dashi don rayuwa abu daya ne wato yayan itatuwa (fruits).  Amfanin yayan itatuwa a jiki ya zarce na sauran nau’ikan abinci wanda ake ci a yanzu. Bari muyi misali da lemo, bincike ya nuna cinye lemo guda daya gabadayan sa harda totuwan ya isa ya kosar da mutum na tsawon wuni daya, wanan yana nuna kenan muhimmanci na yayan itatuwa ajiki.

Photo credit: Pexels.com

Yawancin yayan itatuwa basuda mai, sabida haka basuda kolestara wanda shine sinadarin dayake saka kiba, wanan yana nuna cewa amfani da yayan itatuwa yana rage hadarin samun kiba.

Leman tsami shine dan itace wanda kai tsaye yake kone kiba, duk da yawan amfani dashi yanada nashi matsalolin wanda zamuyi Magana akanasu a nan gaba amma amfanin yafi yawa. Wasu daga cikin amfanonin yayan itatuwa ajiki.

1.      Yayan itatuwa kaman su ayaba, lemo da sauransu suna taimakawa wajen daidaita gudarnar jinni.

2.      Bitamin C sinadari ne wanda yake taimakawa wajen warkewan ciwo da kuma gyara da inganta lafiyan hakori, wanan sinadari ana samunshi ne lemo.


3.      Amfani da kayan itatuwa yana rage hadarin kamuwa da hawan jini da shanyewan jiki.

4.      Cin yayan itatuwa yana kare mutum daga kamuwa da dayabitis (ciwon siga), rage hawan jini, da kuma rage ginuwan duwatsu a cikin koda.

5.      Cin yayan itatuwa yaan rage hadarin kamuwa da cututtuka dasu hada da ciwon zuciya, hawan jini da kuma cutar daji (cancer).


6.      Yayan itatuwa suna kunshe da sinadarai masu saka kuzari da koshin lafiya, amamfani dasu zai samar da wadannan sinadarai ajiki.


7.      Yara yan shekara 2-4 suna matukar bukatar vitamins A da kuma vitamin C ajiki domin samun koshin lafiya dakuma girma dawuri, wadanan sinadarai kuma ana samunsu ne kai tsaye a cikin yayan itatuwa.


8.      Yayan itatuwa suna karfafa garkuwar jikin yaro, bincike yanuna cewa bawan yara kanana yayan itatuwa a kullum yana karesu daga kamuwa da manayn cututtuka.


Yanada da kyau mutane su dinga yawan amfani da kayan itatuwa akoda yaushe kuma suyi kokarin koya wa yayansu cin yayan itatuwan tin suna yara domin su tashi da amfani dasu wanda yanada muhimmanci kwarai dagaske wajen samun isasshen lafiya dakuma kuzari.

No comments:

Post a Comment