Friday, 25 May 2018

Yanda zaka isar wa mace sakon zuciyarka koda baka furta mata kalmar "So" ba.




Photo: pexels.com

Soyayya ko So abu ne da Allah ke sakawa a cikin zuciyoyin mutane wanda mutum bashida ikon sakawa ko cirewa, mutane dayawa idan zaka tambayesu dalilin dayasa sukesan junansa zasu ce maka su ma basu sani ba ko kuma subaka dalilin da bashi bane ba. Wani lokaci namiji yakan kamu da san wata mace ko kuma mace ta kamu da san wani namiji amma yanda zasuyi su isar da wannan sako na zuciyarsu yana zame musu matsala.

Wasu sukanyi karfin xuciya su isar da sakonsu da kansu, wasu kuma sukan aika dan sako wasu kuma sukan nemi lambar waya da sauransu, amma kafin yakai ga bayyana sirrin zuciyarka/ki akwai hanyoyi da za’abi afara isar da sakon zuciya kafin furta da baki. Wadannan hanyoyi zasu taimaka wajen isar da sakon zuciya tin kafin a furta abinda ke cikinta, kuma suna share hanya da saukake isar da sakon zuciya.

1.      Hada ido (eye contact)
Yawan kallo ko hada ido da wacca kake so zai aika wani sako cikin zuciyarta tasan cewa lallai akwai wani abu ataka zuciyar, mata nada kau dakai, zatayi Kaman bata san kana kallonta ba amma tasani, karka damu da wannan kawai duk lokacin da zaku hadu ko zaka ganta ka tabbata ta gani kuma ta gane kana kallonta.


Photo: pexels.com

2.      Murmushi.
Murmushi abu ne mai matukar tasiri a zuciya, murmushi yana sanyaya zuciyar duk wanda aka yiwa shi, duk lokacin da zaku hadu da wacca kake so ko kuma wanda kikeso koda daga nesa ne sai kayi mata murmushi wanda zai shiga har cikin zuciyanta, indai zataga kamata murmushi to tabbas itama  zata maido maka da murmushin daga irin haka zukatan ku zasu kulla abota tsakaninsu batare da sunyi shawara daku ba.

3.      Murmushi da kallo
Bayan kana yi mata murmushi kuma ka tabbata tasan kana kallonta, to sai kafara hada mata duka biyun tare da gaisuwa koda daga mata hannu ne wanan ma yawadatar, kallo tare da murmushin hade da gaisuwan zan tabbatar mata da duk wani shakku datake dashi a zuciyarta. Bin abin ahankali daki daki din bayan kallo sai  murmushi sai kuma hada mata duka biyu hade da gaisuwan lokaci daya yanada matukar muhimmanci, mata a tankware suke sai kabisu ahankali sanan zaka samu abinda kakeso, wata idan kanuna mata alamu kai tsaye  na  kake to ita kuma bazata amince dakai ba tin kafin ma ka furta, amma idan ka bi ahankali sai zuciyarta ta kamu da sonka ko bata shirya ba. Amma wanan bayana nufin idan kanuna ma mace kana sonta bazata amince dakai ba, wasu ma furtawa suke kai tsaye kuma a amince dasu, amma bi ahankali din yafi isar da sakon har cikin xuciya.


4.      Tsafta da shiga mai kyau.
Tsafta da kuma saka sutura mai kyau suna da matukar tasiri wajen jawo hankalin mace, kada ka yarda taganka da a cikin kazanta koda sau daya ne, Allah yayi mata masu san ado, to duk namiji dayakasance mai tsafta mai ado babu shakka zai zama yanada kima a wajen ya mace, duk wacca ka tinkara da Kalmar so zaiyi wuya ta ki amincewa, koda Allah baisa zata amince dakai ba jininku ne kawai bai hadu ba amma bawai sabida bakayi bane.

Photo: pexels.com

5.      Kirki da kyautatawa.
Zuciya tana son mai kyautata mata, yawan kyautata mata zaisa zuciyarta taji tanason ka koda baka furta mata kalmar soyayya ba, amma wannan zai zama sai kana magana da ita ko kuma akwai wata alaka datake hadaku, idan babu sai kayi kokarin yanda zaku dinga magana da ita harka samu daman nuna mata kirkin ka da kuma kyautatanwanka gareta.

6.      Lambar waya
Bayan kun fara gaisawa saika tambayi lambar wayarta dakanka ba kasamua wani wajen kasamo ba, zuciyoyinku sun riga sun kulla kawance ta hanyar kallo da murmushi daka ke ta aika mata, zuwa ka tambayi lambar waya zaisa ta kara tabbatar wa akwai wani sirri a cikin zuciyarka kuma bazata wani bata lokaci ba wajen baka lambar tata domin taji wanan sirri.

7.      Kula
Bayan kun fara magana kuma kuna gaisawa, abu nagaba dazaka shine nuna kula agareta, kanuna ka damu da duk wani abu daya shafeta, ka dinga nuna damuwarka sosai ga duk wasu matsaloli nata. Haka zaisa zuciyarta taji ka damu ita kaine wanda zata dinga bayyana wa duk wani abu daya dameta.

Wadanan abubuwa su zasu saka zuciyarta zataji takamu da sanka batare da tayi shawara da ita ba. Duk lokacin da zaka furta mata Kalmar soyayya bayanda za’ayi taki amicewa dama jiran wanan lokacin take.

Karanta: yanda za'ayi hira da yarinyar kasa takamu da sanka





No comments:

Post a Comment