Tuesday, 29 May 2018

Son maso wani..... hanyoyin da zaka cirewa kanka son maso wani

 
Photo credit : Pexels.com
Bahaushe yace son maso wani koshin wahala. Babu wani abu mai wahala da cin rai irin ka kamu da son wanda kasan bazaka taba iya samun soyyarsa ba. Wasu kan shiga dmauwa mai yawa idan basu samu amincewar wanda suke so ba.

Bai zama dole ka fahimci wanan maganan ba ko kuma wani ma zai dauke ta da wasa har yaga kaman wanan bai kai ayi magana akansa ba, amma duk lokacin da ka samu kanka aciki zaka fahimci irin damuwan da mutum yake shiga idan haka ta faru.

Anan munyi bayani akan hanyoyi 10 dazasu taimaka maka/miki wajen rage damuwar da zaka shiga idan bukatar soyayyarka bata samu amincewa ba.

-          Kada ka wuce gona da da’iri: kasawa ranka cewa kawai zaku cigaba da rayuwa, anan abinda nake nufi shine kada kabari gigin so yana dibanka wajen yin abinda ba’a saka kaba. Idan aka gwaleka na tabbatar bazakaji dadiba musamman ace wanda kakeso ko kikeso na yayi miki.

-          Kada karika tambayoyin da kasan amsarsu bazasuyi maka dadiba: tambayoyi irnsu zaki ko zaka iya sona? Waye saurayinki ko wace budurwarka? Zaki ko zaka iya soyayya dani? Wandan nan tambayoyi duk kasan cewa amsoshinsu bazasu taba yi maka dadi. Saboda kasan wanda kake mikawa tambayoyin bazai taba sonkaba.


-          A lokacin da kashiga damuwa to ka ruga zuwaga abokanka: duk sanda kasami kanka a radin son maso wani to babu abinda zai dauke hankalinka fiyeda gudummawar abokanka ko kawayenki.

-          Kada kakai kanka inda ranka zai baci: anan ina nufin ka gujewa duk wani yanayi ko wani guri da kasan abin son naki ko naka zai kasance shida wanda ko wacce yakeso. Misali idan ida za ayi wani taro kasan zasuje kuma tare da wanda sukeso zasuje, to abi mafi sauki kayi ko kiyi zamanki a gida. Zama a gida ka kalli TV ya fiye maka kallan mayinka shida wani.

-          Kayi kokarin rage haduwa daita:  koda ace ganinta nasaka farin ciki, wannan farincikin na dan lokacine domin idan zaka gansu na tsawon minti 10 to zakayi bakin ciki na awa 24 saboda kasan bazaka taba samunsuba. Ina amfanin ganin abinda yafi karfinka. Kayi ko kiyi kokarin guje musa a hankali zaka iya mantawa daita ko zaki iya mantawa dashi.

-          Kasami wata ko wani: duniya cike take da damammaki, idan wani yakika to wani zai soka. Kayi kokarin samun budurwa wacce zata soka, idan tafara nuna maka soyayya bazakasan sanda zaka manta da waccen ba, a hankali damuwarka zaka dauke zaka koma rayuwa ingantacciya.


-          Kafadi abinda yake ranka batare da saran samin wani abu ba: kafada ko ka ki fada masa cewa ka kamu da sonta ko kin kamu da sonshi, koda bazata sokaba. Dazarar ka amayar da abinda ke ranka zaka sami nutsuwa koda kuwa ba’ace ana sonkaba.


Wadanan kadan Kenan daga cikin hanyoyin dazaka rage damuwar daka shiga a dalilin son wata ko kika shiga a dalilin son wani.

No comments:

Post a Comment