Friday, 25 May 2018

Sinadarin yayan itacen dayake maida tsohuwa yarinya



Photo: Pexels.com

Mata da yawa suna kashe kudadensu wajen siyan mayuka na gyaran jiki da gashi da sauransu wanda lokuta dayawa hakan yakan haifar da matsala a fata. Mata sukan siya mai tsada sabida suyi haske wanda a wani lokacin ba’a samun biyan bukata ko kuma samu hasken wanda aba irinshi ake so ba alhali kinada maganin abun awajenki koda yaushe.
Ana kashe kudi wajen gyaran gashi sabida yayi kyau yayi tsawo amma lokuta dayawa zakaji mata suna korafin sunyi amfani da mayuka dayawa na gyaran gashi basu samu biyan bukata ba alhali kullum kina amfani da maganin gyaran gashin bakisani ba
Akan sha wahala wajen neman maganin fata da sauran matsaloli dasuka daganci fata ashe maganin yana wajenmu.
Leman tsami shine sinadarin da amfaninshi yawuce yanda ake tsammani, kwanaki munyi bayanin amfanonin leman tsami ajiki wanda mun maida hankali wajen amfanoninsa ne ajiki da kuma wajen samun lafiya, yanxu zamuyi bayanin amfanoninsa wajen gyaran jiki da maida tsohuwa yarinya.
1.      Wajen kara haske
Shafa leman tsami kullum a fiska idan zaki kwanta zaisa fiskarki tayi haske tayi kyau sosai, bakaman sauran mayuka na bleaching ba leman tsami abune daga Allah (natural) wanda bazai bada wani matsala ba ajiki. Mata dayawa sun gwada sun tabbatar da leman tsami yaan gyara fata yasa fiska tayi haske kuma bashida wani matsala. Koda kin shafa bakiga canji ba kicigaba da shafwa kishafa na misalim sati biyu tabbas zakiga canji.

2.      Gyaran gashi
Ana amfani da ruwan leman tsami wajen gyaran gashi, zaisa gashi yayi kyau yayi sheki. Sannan kuma ana amfani dashi wajen maganin makeron kai, zubewan gashi da duk wata matsala data shafi gashin.

Photo: pexels.com

3.      Gyaran fata
Ana yin magani na fata da duk matsalolin dasuka shafi fata da leman tsami, idan aka shafa ruwan Leman tsamin a fata yana rage zafin rana kuma yana maganin kyasbi da sauransu. Ruwan na leman tsami yana amfani wajen cire tsufa da tattarewar fata gami da maida tsohuwa yarinya. Shan ruwan leman tsamin hade da ruwa da zuma yana sa fata tayi subul-subul tana sheki.`       

4.      Maganin kuna
Shafa ruwan leman tsamin a wajen da aka kone yana batar da tabon kunan da rage radadin da akeji na kunan.


5.      Fararen hakora
Idan kana amfani da ruwan leman tsami wajen wanke baki zaisa hakora suyi haske sosai, idan hakan ma bazai samu ba zaka iya diga ruwan akan makilin(tooth paste) sai awanke baki dashi zaisa hakora suyi haske kal-kal.

6.      Goge dattin fiska
Shafa ruwan leman tsami musamman idan za’a kwanta yana goge duk wani datti na fiska, fiska zatayi haske tayi sheki, ruwan leman tsamin yana aikin wanan mai na goge fiska wanda ake kira da turanci (cleanser).



No comments:

Post a Comment