Tuesday, 29 May 2018

Muhimman abubuwa da yakamata kasani akan Adam Zango, yawan matan da ya aura dasauransu.


 
Photo credit: Balancy
Jarumi Adam zango babban jarumi ne wanda indai kana maganan sanaar film na Hausa dole sai kayi Magana akanshi, jarumi ne a masana'antar film ta kannywood wanda ya bada gudumawa sosai a cikin masana’antar ta fim din hausa wato Kannywood. Wanan jarumi bai tsaya a fitowa cikin fim ba kawai yakasance yana shirya fim kuma yana bada umarni.  A bayan harkar fim jarumi Adam Zango yana wakoki na hausa wanda yafi karfi a wakokin gayu, kuma yana wakoki da rayuwa da fadarwa da sauransu.

Akwai labarai dayawa da aka wallafa akan Adam Zango da rayuwarsa da iyalansa a shafuka dayawa wanda wasu sun kasance gaskiya wasu kuma ba gaskiya bane, a wanan zamuyi bayani akan tarihi da iyalai da rayuwar Adam Zango.

Takaicaccen tarihin Adam Zango

Asalin sunan Adam Zango shine Adamu Abdullahi kuma an haife shi a daya (1) ga watan oktoba shekara ta 1985 a garin Zango dake jihar Kaduna. Adam zango yafara ne da kida da waka na hausa wanda yake hada ta yanayi na gayu wanda ake kira hausa hip-hop wanda a wancan lokacin kusan shi kadai yake wanan, hakan yasa yasamu farin jinni sosai ganin ya kawo abunda babu shi.

Ganin yanda abubuwa suka cigaba Adam zango ya yanke shawarar shiga harkar fim, Adam zango yafara fim ne a matsayin karamin jarumi, Adam zango bai dade da fara fim ba yasamu karbuwa sosai a wajen masu kallon fim din hausa har yazamana ana hada shi da manyan jarumai na kannywood irinsu Ali Nuhu da dai sauransu.
Photo credit: Daily Trust


Iyalan Adam Zango

Adam Zango ya auri matarsa tafarko a shika dake Zaria dake jihar Kaduna, sunanta Aisha kuma sun haifi yara dayawa tare da Adam Zango.

A shekara ta 2013, Jarumi Adam Zango ya auri jarumar da ta fito a fim din NAS, wato Maryam Abdullahi Yola a lugbe dake garin Abuja.

Amma kafin auren Jaruma Maryam Abdullahi, anyi hira da Adam Zango inda ya bayyana cewa yanada wata matar kafin auren Aisha hakan yanuna cewa Adam Zango ya auri wata matar kafin Aisha.

A shekara ta 2015, Adam Zango ya auri wata yar kasar Kamaru mai suna Ummu kulsum. Aurensa da Ummu kulsum yakasance sirri wanda yabawa masoyansa dakuma sauran yam fim mamaki ganin yanda abun yakasance a boye babu wanda yasamu labari, sun sami haihuwar ya mace da ummu kulsum wanda aka saka mata suna Murjanatu.

Adam Zango ya auri mata dayawa, wasu daga cikin abokanan aikinsa ma sun bayyanna cewa basu san adadin  yawan matan daya aura ba.

Mujallar Fim magazine ta bayyana cewa Ummu kulsum itace matarsa ta karshe kuma da ita suke tare a yanxu. Anga hotunan su da shi daita da jaririyarsu a shafukan sada zumunci na jarumin, hakan ya jawo cece kuce dayawa.

No comments:

Post a Comment