Shin ka sami sabani
dakai da budurwar ka har ya kaiku ga rabuwa? Shin kaya kokarin ganin cewa kun
shirya amma hakanka yaci tura? Karka damu domin yanzu kayanka ya tsinke a
gindin kaba. Yau zan sanar dakai yanda zaka shawa kan tsohuwar budurwarka ku
dawo ku cigaba da soyayarku kamar yanda
kuke kafin samun matsala.
Photo credit: Pexels.com |
Amma kafin nan zan baku dan gajeren labara. Yan watannin da suka wuce wani dan uwa yasami sabani shii da budurwarsa, har takai ga tayi fushi ta rabu dashi, ta daina daukar wayarsa bata amsa text message idan yayi mata. yashiga damuwa matuka. Amma yayi nasarar shawo kanta bayan da yayi amfani da wasu sirrika da wata yar uwata tabashi. Wadannan sirrika kuwa sune:
Waye yafara rabuwa da
wani a tsakaninku: wannan shine babban abin dubawa acikin al’amarin, idan kai
kafara rabuwa da ita ba itace ta rabu dakaiba to wannan yafi wahala akan ace
itace ta rabu dakai. Aikin zaizamo maka mai sauki idan itace ta fara rabua
dakai. A wannan bayani zanyi maganene akan idan iatce ta fara rabuwa dakai.
1. Kayi kokarin fahintar
meyasa ta rabudakai, anan kaza tambayi kanka wai shin tafara soyayya da wanine,
kokuma wani halina ne bataso. Amsa wadannan tambayoyin shine abu na farko da
zai baka damar fuskantarta domin neman sulhu.
2. Kada kacika damunta
akwanakin farko na rabuwarku: a yan kwanakin farko na rabuwarku baikamata ka
takura mata da waya ko zuwa gidansuba. Domin a wannan kwanakin tana cikin yanayi damuwa da bacin ran
abinda ya hadaku. Idan kuma wani sabon saurayi tayi wanda yasa ta rabu dakai to
tana cikin shaukin sonsa. Zaka bata hutu
na kamar sati uku zuwa hudu.
3. Ka gyara wasanka:
bayan hutun daka bata, sannan kuma kagano dalilin dayasa ta rabu dakai, abi
nagaba shine sai kayi kokarin canja halayya kokuma duk wani abu dakasan shine
sandiyyar rabuwarku. Kayi kokari wajen ganin cewa tasan ka canja.
4. Kada kasameta idan
tana tare da wani namijin: kayi kokarin samunta daga kai sai ita kanemi tabaka
dama ku tattauna. Bawayewa bace wai don kasami yarinya kayi mata Magana agaban
saurayinta.
5. Kafara a hankali:
bayan tsahon lokaci da kuka dauka bakwa tare, idan kasami damar yimata Magana to
kafara kamar a ranar kafara saninta. Kayi mata kalamai kamar wata sabuwar
budurwa kakeson tsarawa. Idan kaga tasaki jiki dakai to sai katambayeta kanaso
takara baka dama.
6. Kaziyarceta a
gidansu: idan kaga cewa kadan fara samun fuska to kayi kokarin zuwa gidansu
domin ka tattauna makomar son da kake mata. Kada kacika matsa mata idan tace
kada kazo, kabita a hankali har kasamu ta amince.
7. Abu na karshe idan
duk kayi iyaka kokarinka wajen ganin kashawo kanta amma taki amincewa to dan
uwa duniya ai cike take da marmaki. Idan wani yaki da wuta ta kika da wuni wata
ai zata soka da shekara. Sai kayi mata fatan alheri. Allah ya hada kowa da
rabonsa.
No comments:
Post a Comment