Thursday 31 May 2018

Abubuwan da suke canzawa a rayuwa bayan aure



Aure wata alaka ce da ake kullawa tsakanin namiji da mace wadanda dukansu mutane ne dasuka taso a wurare mabanbanta, kuma kowannensu yanada irin tsarin rayuwarsa da yanayin yanda yake tafe da’ita, bayan anyi aure kuma za’azo a zauna a guri daya. Sai dai bayan auren dole wasu abubuwa zasu canza ga ma’auratan sabida yanzu rayuwarsu tana jone da juna dole kowa yayi abunda zai farantawa dan uwansa kuma yayi kokarin gujewa duk abinda yasan zai kawo matsala a zamantakewarsu. Rashin sanin cewar abubuwa zasu canza ko kuma kin amincewa da canjin yana kawo matsaloli masu tarin yawa a aure, shi yake sa kaga wani auren bai dade ba ya mutu ko kuma ba’a jin dadinsa. Munyi bayani akan wasu yan canje-canje da ke iya faruwa bayan anyi aure

Photo credit: Pexels.com

Yanayin zamantakewa

Lokacin da kukayi aure rayuwarku zata zama ta ta’allaka data juna, kome kake son yi sai ka nemi yardar dan uwanka, misali duk yarda mace take son ta ci wani abu sai mijinta yazama yanaso, idan yakasance bayaso dole ta canza ko kuma ta dafa masa wani abun.

Idan kaya zaki sa sai kin duba irin wanda mijinki yake so, bakaman lokacin da bakiyi aure ba duk abinda kika daman sakawa shi kike sakawa.

Haka shi namiji, duk abinda kakeso kayi ko ka siyo sai matar ka tanaso, misali ko riga ka siya idan matarka tace bai mata kyau ba acanzo haka zaka canzo, bakaman da ba da bakada mata kome kaga daman sakawa shi kake sakawa.

Duk wani abu dakasan kafin kayi aure kakeyi to kasani cewa bayan kayi aure kasamu abokiyar rayuwa to lalle wannan abu zai iya canzawa.

Tsarin rayuwa

Abubuwa dayawa na rayuwa dole su canza bayan aure, yanayin yanda kake kula yammata ko yanayin yanda kike kula samari dole ya canza bayan aure sabida yanzu ke/kai yanzu kana da aure.
Idan kai al’adarka kana kaiwa karfe 12 na dare a waje kafin kayi aure, bayan kayi aure dole ka canza ka dinga dawowa dawuri sabida ka ajiye wanda take jiranka a gida wato matarka. Rashin dawowarka zai jawo matsaloli dayawa na zargi da sauransu wanda kafin kayi aure musamman idan kai kadai kake zama babu wanda zai damu da ka dawo dawuri ko baka dawo dawuri ba.
Photo: pexels.com

Dole ku dinga nesantarda waya da duk wani abu dazai dauke muku hankali idan kuna tare, mazaje dayawa suna samun matsaloli a cikin aurensu sabida bawa waya dukkan hankalinsu, wani zakaga zai rike wayarsa yayi ta dannawa bayan matarsa tanayi masa magana, ko kuma kaga mata mijinta yana mata magana amma hankalinta nakan wayarta, hakan yana jawo matsala sosai a zaman auratayya. Sabida haka indai kayi aure to dole ka rage lokacin da kake batawa akan waya da komfuta da sauransu musamman idan kana gida tare da matarka haka kema mata dole kibawa miji dukkan hankalinki lokacin dakike gida tare da mijinki.

Ra’ayoyinku dole su canza, bincike ya nuna cewa miji yana canza wa matarsa ra’ayi haka zalika mata tana canzawa mijinta ra’ayi, misali idan mijinki ma’abocin kallon wasan kwallon kafa ne kuma yana da kungiyar dayake goyon baya to idan kinason ki dinga jindadin zama dashi musamman lokacin dayake kallon wasa kizama kema kina goyon bayan jungiyarsa, kema dole ki hakura a cusa miki san kallon wasan wanan misali ne kawai bai zama dole yakasance hakan ba, amma tabbas dole ki zama ra’ayinshi shine naki.

Haka miji, misali wani lokaci zakaga namiji yanada zabi na kalar dayakeso na kujeru ko fentin gida, to indai kanada mata dole sai dai kabata zabi kuma kaso wanan zabin nata, dole dai ra’ayoyinku su zama iri daya don samun fahimtar juna.

Sadaukarwa

Dole ne sai ka koyi sadaukarwa, lokacin da bakada aure ko baki da aure zakaga duk abunda kaga dama shi kakeyi kuma a kowani lokaci, bayan aure dole bukatar iyalanka su zasu zama farko sai naka.

Karamin misali idan kanada dubu hamsin (50,000) zakayi wani abu da’ita, sai matarka ko kuma iyalanka suna da bukatar siyan kayan amfanin gida to abun da yakamata anan shine ka biya mata nata bukatar tukun sanan daga baya sai kayi taka inda hali, wanan shi ake nufi da sadaukarwa.

Wani mai gidan zakaga yasiyo nama tsire ko balangu ko kaza, sai kaga daki zai shiga yaci yakoshi tukunna sai ya rage sai ya kira matar tazo ta dauka, in ka tabashi yacema shi yake samo kudin ai, kudinka nata ne nata naka ne duk da wasu mazan bazasu yarda da haka ba, to wanan bai dace ba, abunda yadace anan shine idan kasiyo abu sai ka kawo ka bata ita taci takoshi sanan ka dauki sauran ko kuma kuci tare.

Wadanan kadan kenan daga cikin yan canje-canje da mutum zai iya gani a rayuwarsa bayan aure, saninsu da yarda da su zaisa idan mutum yagansu zai san da su kuma zai san yanda zai tafe dasu kuma zakaga baza’a samu wata matsala ba a zamantakewar auren.

No comments:

Post a Comment