Thursday 31 May 2018

Hanyoyi 10 da zaka gane cewa tana sonka amma ta kasa fadamaka



A wasu lokutan mace takan tsinci kanta a yanayi na so da kaunar wani saurayi amma sobada kunya da allah ya halinci ya mace da ita bazata iya budar baki ta fada masaba. A wannan rubutu zan sanar da kai wasu sirrika da idan akami  kaso mafi yawa daga cikinsu to babu makawa cewa ta sonka. Kaikuma ya rage ya naka ka dauki mataki nagaba.
Photo credit: Pexels.com

1. Tana son yimaka Magana a kowane lokaci. Zaka fahimci hakane idan kaga a kowane lokaci dama ta samu takanyi kokarin ganin tayi maka Magana

2. Tana jin kunyar hada ido dakai. Wasu matan zakaga sun tsoron hada ido kuru kuru da wanda sukaso. Wasu kuma abin bah aka yakeba. Saboda haka sai kayi kokaringano a wannne fanni ita ta fada.

3. Bata son kana mu’amala da wasu matan. Zaka iya gano haka idan misali a makaranta kuke, duk sanda wasu matan suke  tare dakai to zakaga ranta ya far abaci, kokuma tabar wajen dakuke baki daya.

4. Kawayenta zasu sanr dakai cewa ta damu dakai. Idan basu sanr dakai da kansuba to kalura da halayyarsu, zakaga duk sanda kazoo wuri sun dan nutsu, kokuma kaga suna yawan yi maka zancen ita yarinyar.

5. Zakaga tana son abinda kakeso. Idan akwai wani gidan cin abinci da kake yawan zuwa to zakaga itama tana yawan zuwa nan.  Idan misali akwai wata waka da kake so zakaga itama tana yawan sauraren wakar.

6. A duk lokacin da kuke tare zakaga tana yawan wasa da yan yatsunta. Wannan wata babba alamace dake nuna cewa tana ra’ayinka.

7. Tana barin duk wani abu da take don ta ganka ko kuma tayi maka Magana.

8. A cikin hirarku tana yawan fada maka bata da saurayi, Wannan alama ce datake nuna maka tana maraba dakai

9. Tana fada maka wasu magan ganu da bai kamata ka saniba. Kamar sirrikanta da dai sauransu.

10. Takanyi fara’a ko dariya idan kayi mata barkawanci.

Karanta: Sirrika 10 da zaka mamaye zuciyarta ta hanyar whatsapp chat.

No comments:

Post a Comment