Dukkan wani mai lafiyayyan hankali yasan cewa karya ba abune mai kyauba. Amma munin karyar yafi idan yakasance masoyane suke yiwa junansu. Amma wasu lokutan rayuwa takan zama mai wahala, a inda daya daga cikin masoyan ka iya tsintar kansa a wani mawuyacin hali. Akwai wasu sirrika da a kowane yanayi duk rintsi kada kibari saurayinki ko mijinki yasansu. Wadan nan sirrika na iya kawo lalacewar zamantakewarku da saurayinki kai harma da mijinki idan kinyi aure.
![]() |
Photo: pexels,com |
1. Cewa kin taba saduwa da wani.
Wannan shine sirri mafi girma da ya kamata kirike dagake sai allah. Domin wannan wani lamari ne daka iya tunzura saurayinki yaji kin fita daga ransa.tattauna mu’amalarki da wasu samrin na baya bazai haifar miki dad a mai ido ba. Idan har takaiku da yin aure toh duk abubuwan da suka faru abaya sai kawai abar kaza cikin gashinta.
2. Cewa bakya son wani daga cikin danginsa
Mata nada wahalar rike sirri, musamman idan abinda basa sone. Toh amma a wannan yanayi yazama dole kiyi kokarin danne kiyayyar taki. Ba wai ana nufin kuma wai sai kin nuna kina son dan uwan ko yar uwar tasaba amma idan har kika bari yagane kiyayyarki a fili tofa hakan na iya komawa kanki.
3. Cewa abokinsa na burgeki
Idan zuciyarki a matsayinki na mutun taji tana son abokin saurayinki toh babu wani matsala a rike wannan a matsayin sirri keda zuciyarki. Ammafa idan bazali iya daurewa zuciyarkiba tofa babu dalin ajiye wannan a matsayin sirri. Kiyi iyaka bakin kokarin karki raba kan saurayin naki da abokansa
4. Cewa wani daga cikin yan uwanki baya sonsa
Zaifi kyau idan har ki boye kiyayyar da wani daga cikin ahalinki sukewa sauranki. Har abada saurayinki idan ya tuno wannan zance to ransa sai y abaci, har zuciyarsa tafara raya masa wasu miyagun abubuwa, babu wani riba da zaki samu don ki fada masa cewa wane baya sonsa.
5. Cewa kinji dadin soyayya da wani
Wata kila kunyi rayuwa mai dadi da tsohon saurayinki, to wannan ba abune da zaki fadawa saurayinkiba. Saurayinki zaiso yaji cewa babu wani saurayi kamarsa a duniya duk da cewa ba hakabane. Kibinne duk wanni sirri da wata rayuwa da tsohon saurayinki a baya ki maida hankali wajen faranta masa raid a kulawa dashe a kowane lokaci.
No comments:
Post a Comment