Farkon fara soyayyarka da yarinya da kake kauna lokacine mai
matukar nishadi, amma kuma yana iya zam lokaci mai tsanani. Saboda a wannan
lokacine ku biyun kuke kokarin fahimtar halayan juna kuma kuke kokarin burge
junanku duk a lokaci guda. Kowa yasan cewa babu wata tsayayyar kaiida na abida
zakafada mata a kwanakin farko na kulla soyyaarku da mosoyiyartaka. Amma akwai
abubuwa guda 9 da yakamata ace kowane saurayi kai harma da dattawan sun guda a
lokacin a kwanakin farko na fara soyayya da masoyiyar taka.
1. Gaggawa
Kabi abubuwa a hankali, baku jima da haduwa. Mafiya yawan
mutane nayin kuskure a yayin da sufara kulla wata alaka ta soyayya da sabuwar
budurwar tasu ta inda suke azarbabin sai abubuwan sun tafi cikin sauri. Kayi
hakuri zaka rika samun cigaba a soyayyarku ammafa sai a hankali. Idan kacika
matsawa da takurawa tofa zaka iya yin biyu babu.
2. Karya ko fafa kamar yanda kukafi saninta dashi.
Kada kasake gigin so ya debeka karika fadin abuwa barkatai
don kaburge yarinya. Idan tafiya tayi tafiya yarinyar nan zata gane cewa duk
zantukan da karikayi mata a baya duk karyane. Hakan zai iya kawo maka raini da
zubewar girma. Ka kulla alakarka da ita
akan gaskiya wanda koda a gaba baka da wata fargaba sobada baka taba mata
karyaba.
3. Bakai ba zancen tsohuwar budurwarka.
A farkon kwanakin da kafara kulla alaka da sabuwar budurwarka
, akwai yuwawar cewa tsohuwar budurwarka na nan a cikin zuciyarka. Kayi kokari
matuka wajen ganin cewa baka kamatata da tsohuwar budurwarka. Kuma kada karika
bata labarin rayuwar soyayyar dakukayi da tsohuwar budurwar taka. Saobada
sabuwar budurwar taka zata kamar har
wannan lokaci baka daina son waccen ba. Fadakarwa ta karshe: karka sake ka
kirata da sunan tsohuwar budurwarka.
![]() |
Photo credit: Pexels.com |
4. Kar ka nuna mata matsanancin so.
Idan kakamu da wani, zakaji kamar cewa kana son kakasance
dashi a kowane lokaci, amma abinda ya fiye maka shine kabashi yar tazara kadan.
Kada kafiya kiranta awaya , kada kacika zuwa gidansu, kada karika tura mata
sakonni ta whatsapp duk bayan mintina kadan
haka na iya rage maka kwarjini a gurinta. Kasani cewa yawan kaya a
kusiwa shiyake rage musu dagaja.
5. Karka watsar da abokanka
Kada kamanta da taimakon da abokanka suka maka a lokacin da
kake cikin halin damuwa, saboda kasamu sabuwar budurwa. Kasani abokanka na nan
tare dakai a kowane yanayi mai dadi ko akasin hakan. Wai shin idan kayi watsi
dasu wane ya baka tabbacin cewa soyayyar taku zata dore.
Karanta: Hanyoyin da zakabi kasace zuciyarta
No comments:
Post a Comment