Sunday, 13 May 2018

Alamomi 10 dazaka gane cewa budurwarka na yaudararka







1. Kana iya matukar kokarinka wajen ganin cewa tana samun kulawa amma bata taba cemaka ta godeba. A kowane lokaci farin cikinta shine abin damuwarka amma kwata kwata bata fahimtar hakan.

2. A kullun kai kadai kake kokarin ganin alakar takara kulluwa. Idan har zaka kadan jabaya to wannan alakar taku zatayi rauni. Abinda nake nufi anan shine ita budurwar taka bata yin ban ruwa a gonar soyayyarku, kai  kadai kadamu da ingantuwar gonar taku.

3. tana yi maka karya a kowane lokaci kasancewar tasan zaka amince da ita. Tana yin amfani da wannan dammar na amincewa da kai da ita wajen yimaka karay rayi wanda suke bata maka rai.

4. tana nuna wasu halaye munana a gabanka duk kasancewar tasan bakaso, saboda tasan babu abinda zaka iyayi. Saboda tasan sonta yagama rufe maka ido.  Zatayi amfani da wannan damar na tsananin sonta da kake wajen wajen ganin ta munana maka.

5. Tana kokarin nuna maka cewa kamar taimaka maka take da take soyayya da kai. Zata nuna maka kamar idan baka tare da ita to kai taka takare. Zata saka karija kamar babu wadda zata soka bayan ita.

6. Tana rokonka fiye da kima batare da kojin kunyaba. Kana matukar kokarin ganin ka buya mata bukatunta amma ita a bangarenta bata wani yunkurin kyautatamaka ko biya maka naka bukatun.

7. Tana kokarin karbar ragamar duk wani lamura na rayuwarka duk da cewa kai baka mata shishigi a cikin al’amuran rayuwarta. Kana bata duk wani yanci day a kamaceta amma ita a bangarenta abin bahaka yakeba. Yanda takeso haka za’ayi.

8. Bata taba nuna cewa ita budurwarkace. Tana amfani ne dakai idan bukatar hakan tataso. Duk dacewa kai ka dauke alakar soyayyarku da muhimmanci amma amma ita tana amfani dakai kamar wata safaya taya, ba’a nemanka saida bukata.

9. Bata yarda ku tattauna makomar soyayyarku a shekaru masu zuwa, abinda kawai tafi damuwa dashi shine yau. Ita kuma makomar soyayyarku kawai abarwa Allah.

10. Tana kushe ra’ayoyinka da tunanin. Haka zalika zatake nuna maka cewa ra’ayinta za’a abi a duk wani abu daya taso dake bukatar ra’ayoyinku.
Alamomi 10 dazaka gane cewa budurwarka na illatka
Shin kataba tsintar kanka acikin duka ko daya daga wadannan? Zaka iya tattaunawa dani a comment section.

karanta: abubuwan da mata sukace maza sun kasa fahinta


1 comment:

  1. Da kyau Waye kai yaya sunanka kamata yayi kabude shafin facebook dan allah inna son number wayanka gata wanan 09033707868

    ReplyDelete