Bayan namiji yafurta wa mace cewa yana sonta yawancin
mata abunda sukeyi shine zata baka dama ne taga yanayin irin halayyarka sai ta
yanke shawarar ta amice dakai ko kuma karta amince dakai. Maza dayawa sukan
zama cikin tinani da kokonton ko sun sami nasarar sace zuciyan mace ta amince
dasu din ko kuma dasaura, hakan yakan sa wasu su zama cikin damuwa sabida
basusan matsayinsu ba. Yawancin lokuta
mace bazata cemaka tana sonka ba ko kuma ta amince dakai sai dai kagane hakan
ta yanayin yanda kuke Magana da sauran mu’amala. Akwai alamu dazaka gane cewa
yarinya tana sonka ko bata sonka. Zamuyi
bayani akan wasu daga cikin alamu da zaga gane cewa lalle yarinya tana sonka.
1.
Kunya
Idan yarinya tana sonka, zakaga tana
kunyar ka, idan kana kusa daita zata zama takasa samu nitsuwa, zakaga tana wasu
abubuwa irin wasa da hannunta, zakaga ta rike hannayenta tana Magana kasa kasa,
kawai zaka lura cewa Kaman bata ma son hirar dakukeyi to bahaka bane alama ce
datake nuna cewa kashiga zuciyanta.
2.
Kallo
Idan yarinya tana sonka, ka faki ido
ka kalleta zakaga cewa tana kallonka, wata idan kuka hada ido zata saukar
dakanta, wata kuma dukda kun hada ido zata cigaba da kallon yan dakiku kadan
sannan sai tayi murmushi takalli kasa
wanan alama ce babba dake nuna zukatanku sun amince da juna.
3.
Murmurshi
da fara’a
Akwai yanayi na murmushi da fara’a wanda
aka saba gani akwai kuma na daban, idan yarinya tana sonka duk lokacin da kazoo
wajenta ko kuke waya zaka fahimci tana farin ciki da magana dakai koda kuwa
bata cewa komai sabida kunya amma zaka fahimci cewa tana fara’a da farin ciki
kuma zakaga tana ta murmushi koda bakace komai ba, kuma bataso katafi ko ku
gama wayan koda bawani magana ta kirki kuke yi ba, wanan alamu ne na kasace
zuciyarta.
4.
Damuwa
dakai
Idan kaga yarinya ta damu dakai idan
bata ganka ba tsawon lokaci kaga ta damu tana nemanka, bayan yan awanni kadan
kaga tana kiranka a waya ko kuma idan baka kirata ba koda ace na tsawon awa 5
ne sai kaga ta damu, wanan jin muryar taka da take yana kwantar mata da hankali
ne. Wanan alamu ne dake nuna lalle tana sonka.
5. Idan
yarinya tana sonka zakaga tana son magana dakai, komai kafada dai dai ne, duk
wani labara dazaka bata na raha zakaga tana dariya koda abun bai bata dariya
ba, kome kafada kuma bazai bata mata rai ba, tana karbar duk wani shawara daka
bata wanan alama ce datake nuna yarinya tana sonka.
6. Idan
kaga kuna tare da yarinya tana baka dukkan hankalinta idan kuna magana, ko
wayarta bata tabawa tabaka duka hankalinta tana sauraron abunda kake cewa to
lalle yarinyar nan tana sonka.
Karanta: Sirrika 10 da zaka mamaye zuciyarta ta hanyar whatsapp chat.
No comments:
Post a Comment