Monday, 14 May 2018

Mata kuyi hattara: kalar maza 7 da bai kamata ki aura ba.


Photo: pexels.com

Kowace mace tana burin ganin ranar aurenta, haka kuma tana burin ganin cewa tasami miji nagari. Duk munsan cewa ba aikiin mace bane neman namijin dazai aureta saboda kunya da al’ada. Amma haka bashi yake nuna cewa kowane irin namili idan yazo sai ki karbeshiba. Ba kowane namiji ne ya dace ya aurekiba yar uwa. Kowanne namiji tara yake ba cika gomaba. Idan kikasamu saurayinki nada kaso mai yawa daga cikin wadannan halayen to yar uwa karki sake ki aureshi.

1 wanda kika gane har yanzu yana son tsohuwar budurwarsa.
Irin wannan mazan zasu nuna miki so matuka amma a duk lokacin da dama tasamu yana kokarin tunawa da tsohuwar budurwarsa ta hanyar kwatantaki da ita. Irin wadannan maza bazasu taba sonki  yanda ya kamataba saboda har yanzu akwai burbushin son tsohuwar budurwarsa a ransa. Kedin kawai manage yake dake.

2 mai wulakanta mata

A matsayinki na mace nasan kinfi kowa sanin halin da mace take shiga idan tasami kanta a hannun mugun namiji. Kin sami labarin yadda wata yar uwarki ko kawarki tasha wahala a hannun mijinta, wannan aikinki ne tun kafin kuyi aure kifara binciken halayensa na Sali ba halayen da yake nuna mikiba. Akwai wasu mazan da halayensu ko kare bazai ciba. Wani zakiga yana dukan mace yana zaginta da dai sauransu. Yar uwa kiyiwa kanki katangar karfe da irin wadannan mazan ta hanyar bincikike kafin ki yarda ki aureshi.

3 Dan mama
Hmmm, nasan zakiyi mamaki. Eh hakan dai nake nufi wata dan gatan mamansa. Shi irin wannan namijin matsalarsa shine idan kike aureshi duk abinda kikayi masa sai yayi miki korafi, wais hi bahaka ya sababa. Ko shi bah aka mama take masaba. Zaki sameshi yaki ya girma ya fara yiwa kansa tunana. Komai ya taso masa kawai abinda zaice miki shine “toh zan tambayi mama” rayuwar aurenki dashi komai mamam ce take kullawa. Shi kwata kwata bashi da ra’ayin kansa. Sanarwa: hakanfa ba ana nufin ki auri auri mai sabawa iyayansa bafa. Sai ki kiyaye.


4 makaryaci
Shi wannan komai na rayuwarsa sai ya saka karya acikinta. Bashida gaskiya a duka al’amuransa. Abubuwa biyu ne zasu faru idan kika sake kika aureshi. Nadaya  zaki koyi karyar daga gareshi, na biyu zaku haifi yaya makaryata fiye dad a babansu saboda ai hausawa nacewa kyan day a gaji ubansa.

5 marowaci
Mutumin da baya taba iya yi miki kyauta duk dacewa yana da hali, toh yar uwa wannan idan kika aureshi zakisha wahala wallahi.shi aure yana tare da bani bani, to wanda baya iya bayarwa tun kafin ayi aure kinsan cewa kokunyi aure bazata canja zaniba.

6 mallam komai komai na iaya
A farkon haduwarki da irin wadannan mazan zakiji yana burgeki saboda saninsa da abubuwa. Abune mai kyau ace saurayin yanada fasaha sosai, yasan abubuwan da baki saniba kuma yana koya miki. Amma abin zai fara damunki idan yafara zakewa wajen nuna miki shifa komai ya iya, yanada wayewa da dai sauransu.

7 mai son kai
a kowane yanayi shi mai son kai masalaharsa kawai yake dubawa acikin al’amuran rayuwa. Babu ruwansa da halin da wani zai shiga sanadiyarsa na kokarin samarwa kansa wani abu. Baya taba fifita bukatar wani akan tasa koda kuwa hakan shine masalaha.


photo: pexels.com

No comments:

Post a Comment