![]() |
Photo: pexels.com |
Leman tsami daya ne daga cikin yayan itatuwa wanda
mutane dayawa basusan amfaninsu a jiki ba ko kuma sun sani amma basa damu da
amfani dashi ba. Leman tsami Kaman yanda sunan yake yanada tsami bakowa zai iya
amfani dashi kai tsaye ba amma kuma yanada wasu sinadarai na vitamins wanda
yasa yazama daya daga cikin yayan itatuwa mafiya amfani a duniya. Mutane dayawa
suna amfani da leman tsami a wajen girki wajen dauke karni, samun flavor, da
kuma amfani a shayi da dai sauransu, amma amfanin leman tsami yawuce haka
yanada matukar amfani wajen inganta lafiya da gyaran jiki.
Ga wasu daga cikin amfanonin leman tsami ajiki:
1.
Rage
kiba
Yawan amfani da lemon tsami yana
taimakawa wajen konar da teba, binciken masana ya nuna cewa shan leman tsami da
ruwan zafi a kullum yana taimakawa wajen rage kiba matuka.
2.
Rage
tsufa
Maimakon kashe kudi wajen maya-mayai
masu maida tsohuwa yarinya, yawaita amfani da leman tsami zaisa fiskarki ta
koma ya yarinya yacire duk wani alamu na tsufa ajikinta.
3.
Kariya
daga duwatsun koda
Leman tsami yanada wani sinari wanda
yake hana ginuwan duwatsu a koda, Yawan amfani da leman tsami yana kare koda
daga duwatsun dake ginuwa acikinta.
4.
Samar
da bitamin C
ss="MsoListParagraphCxSpMiddle">
Bitamin C sinadari ne wanda yake da
matukar amfani ajiki, amfanin shi yahada da kariya daga cututtuka, sanyi, cutar
daji, karfafa garkuwar jiki, rage hawan jini da sauransu. Bitamin c yakasance
sinadari mafi amfani ajiki. Leman tsami yana daga cikin yayan itatuwa da ake
samun Bitamin C ajikinsa.
5.
Warkarda
zazzabi
Shan ruwan leman tsami yana taimakawa
wajen warkarda zazzabi da sanyi ajiki.
6.
Waraka
daga kunan wuta
Shafa ruwan leman tsami a wurin da
aka kone yana warkarda kunan yakuma batar da alamun kuna, sanan yana saukaka
zafi da azaban da akeji a wajen kunan.
Ana amfani da leman tsami wajen
maganin cututtuka dayawa misali, cushewar dubura, matsalolin hakori, matsalolin
makogaro, zubar jini na ciki, kuna, kiba, kwalera, hawan jini dakuma gyaran
jiki da gashi.
Amfanin leman tsami bai tsaya a nan
ba, wasu na amfani dashi ta hanyoyi daban daban dan bukatarsu ta yau da kullum.
Wasu suna hada ruwan leman tsami da ruwa domin amfani wajen wanki sabida leman
tsami yanada karfin cire datti a jikin kaya.
Kanshin leman tsami yana korar kwari irinsu
sauro da sauransu, idan akasaka bawon leman tsamin ko leman tsamin a wurin da
ake samun sauro kanshin zai koresu gabadaya.
No comments:
Post a Comment