Monday, 14 May 2018

Amfanin da shan ruwa kafin kaci komai da safe zaima jikinka

photo: pexels.com


Ruwa abokin rayuwa, dole saidashi zaa iya rayuwa. Bayan sha na bukata ruwa na iya zama magani ko riga kafin wasu cututtuka dazasu iya kama mutum.
Shan ruwa 500ml bayan an tashi daga bacci kafin aci komai yanada matukar amfani ajiki. Tambaya guda daya, Zaka iya awa takwas (8) baka sha ruwa ba? To kwatankwacin wadannan awanni jkinka yake bai samu ruwa ba yayin da kayi bacci na dare. Tabbas bayan tashinka daga bacci jikinka zai bukaci ruwa domin gudanar da al’amura na jikinka.
 Shan ruwa kafin aci komai yana taimakawa wajen wanke hanji da duk wani datti dake cikinta, shan ruwa glass daya da safe zai daidaita aiki na hanji da sauran bangarori na jiki.
Ga wasu amfanonin shan ruwa kafin aci komai dasafe:
1.      Yana samar da ruwa a jiki (rehydration)
A lokacin da ka tashi daga barci ruwa yakare ajikinka koda lita nawa kasha da dare kafin ka kwanta, kana bukatar ruwa kana tashi da safe domin cikinka yazamana akwai ruwa musamman lokacin zafi. A lokuta na zafi ana bukatar adinga shan ruwa sosai da sosai domin samun ruwa ajiki.

2.      Inganta lafiyar Koda
Koda itace take tace duk abunda yashiga ciki ta ware mai kyau da turo marar kyau ta fitsari dasauransu, sabida haka tana bukatar ruwa wajen tace abubuwa. Shan ruwa da safe zai bata daman tace abubuwan dasuka shiga ciki.

3.      Maganin ciwon kai
Kashi tamanin da biyar (85%) na kwakwalwa anyi shi ne da ruwa, rashin ruwa wadatacce a jiki zai iya sa kwakwalwa tadinga samun matsala adinga yawan ciwon kai. Binciken masana ya nuna cewa rashin isasshen ruwa ajiki yana kawo ciwon kai, binciken kuma ya nuna cewa shan ruwa da safe da kodayaushe yana maganin matsalar ciwon kai.

4.      Wanke cututtuka
Lokacin da kake barci jikinka yana wanke duk wani datti, bayan yagama wanke wanan dauda sai ya tara shi waje daya wanda shan ruwa bayan an tashi daga barci kafin aci komai shine zai wanke wannan dauda.

5.      Sanya nishadi
Shan ruwa da safe yanasa mutum yajishi cikin nishadi.

6.      Karfin jiki
Shan ruwa da safe kafin aci komai yanasa karfin jiki, musamman lokacin motsa jiki (exercise). Yayin da kake motsa jiki zufa yana zuba ajiki, to idan aka sha ruwa da yawa dafe zaisa asamu karfin jiki koda zufa yana zuba din.

7.      Sawwake bayan gida.
Lokuta dayawa wasu mutane har dabbobi suna fiskantan matsala a cikin bandaki (toilet).
Shan ruwa da safe da sauran zai sa asamu wadataccen ruwa ajiki yanda abun da akesan fitarwa xai fita cikin sauki.

No comments:

Post a Comment