Wednesday, 30 May 2018

Hanyoyi 10 da zaka mamaye zuciyar mace ta hanyar whatsapp chat.



A lokuta da yawa, maza na yin kuskure inda daga zarar ance sun sami amincewar wacce suke so kawai saisu ajiye makaman yakinsu, su rage kokarin da suke ada kafin su samin amincewarta. Wannan ba karamin kuskure bane. Mata har abada ababen kauna ne, suna da bukatar a sosu, a kaunacesu, akuma yabesu.  Akowane yanayi yakama ace kana neman hanyoyin da zaka burgeta ka kyautata mata indai har kanaso ta cigaba da kasancewa budurwarka. Daga zarar akace tasani wanda zai mata abinda kakasayi to kaifa taka tazo karshe.

A wannan bayani zan baka sirrika 10 dazabi ka burge burge budurwarka kasami kauna da amincewarta duk ta hanyar whatsapp. Idan har kayi amfani da wadannan hayoyi ina mai tabbatar maka babu mai iya kasaka a wajenta.
                           
             
Photo credit: Pexels.com

  • Karkayi kokarin kama da wani: abu na farko da yakamata katuna shine budurwar nan taka tasanka, saboda haka kada kadau halayya ta wani kadorawa kanka. Kaje mata a yanda kake. Idan har takama cewa sai ka kwaikwayi wani to yakasance bazaka kwaikwayeshi dayawa har tageneba. Abinda yasa nace karka kwaikwayi halayyar wani shine, mata nada wani hali na karanta tsofaffin sakonninsu na whatssapp, dazarar tazo kan wani tsohon sakonka zata iya tunawa da raina mata hankalin dakayi.


  • Sunaye masu dadi kona tsokana: sunayi irinsu sweety honey da sauransu sune sunayen da yakama kake kiranta dasu idan kuna charting. Sannan kuma zaka iya saka mata wani suna na tsokana kake kiranta dashi. Misali idan farace zaka iya rika cemata yar fara.



  • Ka rinka yabonta:  mace babu wani abu da takeso fiyeda namiji ya yabeta.idan tayi wani hoto mai kyau yakasance kaine na farko da zaka yabawa kyandatayi, idan kunshi tayima kayaba mata. Abin dubawa anan shine kada yabon naka yazama ya wuce kima, ko tagene cewa kana yabontane kotayi kyau ko batayi kyauba. Indai tayi abinda ya burgeka kayaba mata.



  • Sakon safe: wannan wani sirrine da bakowa yasan shiba, sirrin kuwa shine kullum da safe katura mata sakon soyayya. Amfanin hakan kuwa shine, sakonka shine abinda zata karya dashi wanda zai baka damar kasancewa a ranta tsahon ranar.


  • Karika tura mata sakon voice notes: fasahar sakon voice note ya kara inganta hanyoyin isar da sakon soyayya idan har kayi amfani amfani da ita yanda yakamata. Katura mata sakon soyayya da muryarka a sanyaye a hankali. Wannan zai kara kulla dankon soyayya a tsakaninku. Sannan kaima zaka iya cewa ta turo maka sakon voice note.



  • Kasaka hotonta profile pic dinka: chatting kawai bayasakawa kasami amincewar budurwarka, saka hotonta a profilpic dinka ka iya canja al’amari. Kasami wani hotonta wanda yayi tsananin kyau ka dora kaga yanda zataji dadi.


  •  Kayi kakarin yin gajeran charting: tura mata dogayen sakon ni marasa ma’ana bazai taba sawa ka burgeta. Haka sai dai ya jawo taji kawai taji ka isheta. Sakonninka su zama gajeru masu ma’ana.


  • Kartayi ta ganinka online:  karika dandana mata zakin soyayya, idan taji dadi to sai kadan janye jiki don tayi kewarka. Amma idan kullum tana ganinka a arha to hakan zai rage karsahin soyayyarku. Idan kadandana mata sai kadan buya nawasu lokuta haka zaisa tashiga nemanka ido rife.


          
Photo credit: Pexel.com
  • Karka dade baka amsa sokontaba: wasu mazan sukan danja aji kafin su amsa sakon da budurwarsu ta aiko musu. Haka na matukar batawa mace rai. Nasan zakace ai suma mata basa yin reply da wuri, eh hakane basayi amma ai kai namijine, mata aka sani da jan aji. Kasani akwai maza da yawa da suke son samun irin damar daka samu. Saboda haka kayi amfani da damarka.


  • Karika jaddada mata yanda kake sonta: bayan wasu hirarraki na duniya dakukeyi a whatsapp, abu mafi mahimmaci shine karika jaddada mata yanda kake kaunarta a koda yaushe.



karanta: Yanda zaka gane cewa budurwarka na yaudararka

No comments:

Post a Comment