Haske da kyau na hakora suna kara wa mutum kyau da
kwarjini a idon jama’a ko mace ko namiji. Idan hakoran mutum suna da kyau
zakaga yana nishadi cikin mutane koda yaushe, kowani lokaci zakaga yana cikin
dariya yana washe baki cikin jama’a sabida baya shakkan hakan, amma zakaga idan
hakoran mutum basuda kyau baya san bude baki a cikin jama’a zakaga yana kokarin rufe bakinshi a koda
yaushe sabida rashin kyan hakoran.
Photo credit: Wikipedia |
Akwai mayukan wanda ake siyarwa na hasken hakora amma
wadannan mayuka wani lokaci zakaga basa aiki yanda yakamata wani lokaci kuma
idan anyi sa’a suyi, koda sunyi aiki zakaga kemikals (chemicals) ne a ciki
wadanda zasu iya yiwa mutum illa a hakoran.
Akwai abubuwa na gargajiya wasu daga itatuwa wasu
sinadarai ne daga Allah wadanda zakayi amfani dasu su wanke maka hakora suyi
haske sosai kaman na jariri. Anan zamuyi bayani akan wasu daga cikin wadanan
abubuwa.
Photo credit: Pexels.com |
1.
Gawayi
Abun mamaki ne ga wasu ace gawayi
dayake baki zai sa hakora suyi haske, tabbas hakane, ana amfani da gawayi wajen
wanke hakora suyi haske sosai. Gawayi yana daya daga cikin abubuwan da suka fi
kowanne wanke hakora suyi haske sosai. A cikin gawayi akwai wani sinadari wanda
shine yake wanke hakoran. Daga yanzu idan aka siyo gawayin girki sai a rage na
wanke baki.
2.
Bawon
ayaba
Mutane dayawa bayan sun ci ayaba ba
abun da sukeyi da bawon ta sai dai su yar, bawon ayaba yanada amfani sosai idan
anyi amfani dashi wajen wanke hakora, zai sa suyi haske suyi kyau. Bayan ka
bare ayaba zaka iya ajiye bawonta kayi amfani dashi wajen wanke hakora yanada
matukar tasiri.
3.
Gishiri
Gishiri sinadari ne wanda yake da
matukar amfani, amfanin shi yawuce ayi girki kawai, ana amfani da wajen wanke
hakora, amfani da gishirin yana kashe wannan dattin kalar ruwan dorawa dayake
fitowa a hakoran wasu mutane, yana wanke kwayoyin cuta a hakora kuma yana saka
hakora suyi fari suyi haske.
4.
Leman
tsami
Leman tsami abu ne da yake da matukar
amfani a jikin dan adam, ana amfani dashi ta hanyoyi daban daban a jikin dan adam
wajen inganta lafiya. Daya daga cikin amfanoni na leman tsami shine wanke
hakora, Amfani da ruwan leman tsami wajen wanke yana kashe kwayoyin cuta, ya
karfafa hakora kuma yasa suyi haske matuka.
5.
Man
kwakwa
Amfani da man kwakwa wajen wanke
hakora yanasa hakora suyi haske, bayan haka yana wanke hakoran daga cututtuka
yakuma saka kamshi mai kyau daga baki.
Karanta: Amfanin leman tsami wajen kiwon lafiya
Karanta: Amfanin leman tsami wajen kiwon lafiya
No comments:
Post a Comment