![]() |
Photo credit: Pexels.com |
Wani
babba malami a fannin nazarin halayyar dan adam Albert mehrabian
yace kaso 7 cikin dari ne na hanyoyin sadarwa tad an adam yake
bukatar furuci. Akwai wasu mahimman sakonni a yanayin yadda muke sadarwa
sakaninmu. Idan har dan adam yana so yaji dadi rayuwa to akwai bukatar yasan
wannne irin sakonnine wadannan.
Babba
abin dubawa anan shine mu’amala tsakanin mace da namiji. Mafi yawan kaso daga
cikin matsalolin da ake samu a zamanta kewar mace da namiji na faruwa ne
sanadiyar hanyoyin da suke amfani dasu wajen isar da sakonni.
Maza a
mafiya yawan lokuta suna amfanine da harshensu wajen isar da sakon da sukeso su
isar. Amma fa mata abin bahaka yakeba agunsu domin suna da hanyoyin
isar da sako bila adadin wanda maza keta faman korafi sun kasa
fahimta.
Babban da
namiji zai kula dashi a yayin da mace take Magana, yayi la’akari da kalaman
bakinta sannan ya lura da yanayin jikinata a lokacinta da take Magana domin
suma suna isar masa da wasu sakonni.
Karanta
wannan gajeriyar tattaunawar tsakanin mace da namiji domin kafahimci inda na
dosa.
1. Ta
cika korafi ko mita.
Namiji: meyasa
akowane lokaci take min mita da korafi. A kullum neman laifina
take don tayi korafi kamar yadda ta saba.
Mace: ina sane nake
masa haka. Kawai ina so naga ko yana sona da gaske, kuma na gwada
naga
yaya
juriyarsa take.
A lokuta
da dama ko macen ko namiji akwai hanyoyin da suke amfani dashi wajen gwada
juriya da karfin son dad an abokin mu’amalarsu yake musu. Maza sun fuskanci
matsala wajen kasa fahimtar cewa mita da matansu keyi kawai dabi’a ce wacce sai
sunyi bakuma zasu iya dainawaba. Ida har maza zasu fahimci haka to zamansu
zaiyi dadi.
2. Kasa
fahimtar mai take son cewa (kamar da wani sabon yare take Magana)
Namiji: kina
yimin Magana ki soko wannan ki soko wancen, wai me kike son fada ne
Mace: ya kasa
fahimtata, shi kawai so yake afadi abinda ransa yake so.
A kowanne
mu’amala ta zamatakewa tsakanin mace da naji, suna amfani da yare biyune. Na
daya shine yaren da ake Magana kai tsaye, wanda maza ne suka cika amfani
dashi. sai kuma yare mai kwana kwana wanda shi kuma mata ne suke amfani dashi.
Maza sukan yi Magana ne kai tsaye domin su isar da skon da suke son isarwa
domin su tafi zuwa abu nagaba. Mata kuwa sukanyi tasu maganar ne domin kara
kulla wata mahada tsakaninsu da wanda suke maganar dashi, domin kara kulla
alaka tsakanin maganarsu ta jiya da ta yau. Domin haka su sunfi damuwa da
shauki ko fishin da zasu sakaka idan suka maganar fiye da gundarin kalmomin
nasu. A duk lokacin da kaga mace tana farin ciki da maganar data fada to bawai
kalmomin da tafada ne suka faranta mataba face irin face yanayinda ta sakaka
sanadiyar fadar maganar.
A duk lokacin
da mace ta fada maka wata magana mai dadi ko mara dadi, kawai kayiwa kanka
wadannan tambayoyi:
i.
Wane sako take son isarwa da take fadin wannan maganar?
ii.
A wane yanayi take wannen zancen?
iii.
Wane yanayi ka tsinci kanka lokacin da tayi wannan maganar?
Sanar da ita.
karanta: kada kisake kibar sarayinki yasan wadan nan abubuwan
No comments:
Post a Comment